YABON GWANI......
Farkon baitin Ilahi zan ambata,
Masanin sirrin dukan nagarta,
Mai bayarwa gami da ƙari.
Rabbi lamunce na tsara baituka,
Ga gwanin nan na mu mai hazaƙa,
Musaddam M Idriss a tsari.
Ja mu je Oga abun fahari,
Ɗaya tilo ka wuce garrari,
Shugaban Powa bugu da ƙari
Roƙona gun Ilahi mai sama,
Kullum ka zamo cikin ƙirama,
Gun Al'umma ka zamma nuri.
Rubutawa: Muhammad Musa Tika
30th-10-2020
0 Comments