An bayyana gwarazan gasar powa mai jigo akan "Talauci"

Alƙalan gasar ƙungiyar marubutan nan mai suna Potiskum Writers Association (POWA) sun fitar da sakamakon gasar kungiyar mai jigo akan 'TALAUCI'. 

Sanarwar sakamakon wadda aka bayyana a shafin yanar gizo na ƙungiyar na ɗauke da jerin sunayen marubutan da labaransu suka yi zarra a kakar gasar. 

Wasu Labarai masu alaka da wannan:

● Kwamitin alƙalai sun bayyana marubuta shiga da suka yi nasara a gasar gajerun labaran powa

Ga dai jerin sunayen marubutan da suka lashe gasar kamar yadda aka wallafa a shafin kungiyar;

1. Rabi Garba Tela a mataki na ɗaya fannin gajerun labari.

2. Hauwa'u Adam Suleiman a mataki na biyu fannin gajerun labarai.

A fannin rubutattun wakoki Murtala Uba Mohammed ne yake a mataki na ɗaya yayin da Ibrahim Khalil ke biye da shi a mataki na biyu.

Sauran labaran sun gaza wajen cika sharudan gasar kamar yadda sanarwar ta nuna a shafin kungiyar. Sai dai kuma kungiyar ta bayyana cewa su ma wadanda ba su yi nasarar ba za a ba su takardun shaidar shiga gasar.

A mako mai zuwa ne ake sa ran kungiyar za ta saki jigon da za a fafata gasar watan Nuwamban da zamu shiga.

Reactions
Close Menu