Ma'anar Depression da bayanin yadda ake gane mai dauke da ita


Idan akwai wata kalma ta harshen Turanci da a 'yan shekarun nan ta shiga bakunan mutane a zantukansu na yau da kullum, musamman idan wani al'amari marar daɗi dake matuƙar cike da abin al'ajabi ya faru to ba ta wuce jin ambaton kalmar nan mai suna "Depression" . Sai dai wani gagarumin abin lurar kuwa shi ne dukda  sake yawaitar mutanen da suka san ita wannan kalma da ake daɗa yi, a na iya cewa ɗaukacin masu amfani da ita ɗin musamman a yankunan ƙasashen Hausawa ba su san haƙiƙanin abin da ita wannan kalma take nufi ba. Yayin a ɓangare guda ɗin kuma dai harwayau, ƙalilan ɗin da suke da 'yar masaniya akan nata kuma wato waɗanda ke iya danganta ta da faruwar mummunan al'amari suke ɗaukarta a matsayin kalmar dake nuna "halin damuwa" ko kuma ma dai fassarata kai tsaye da sunan "Damuwa".

Wannan dalili kuwa shi ne mafarin ɗora tubalin da yasa da zaran an ambaci "Depression" sai ka ga hakan ba ya ɗaɗa mutane da ƙasa sam saboda a normal situation , jama'a na da tunanin cewa ai damuwa ba wata aba ba ce ta tayar da hankali saboda kowane Ɗan Adam dama ba a rasa shi da damuwa irin tasa. Inda har wasu kan bada misalai masu kama da cewa; wani damuwarsa abin da zai ci ne, wanin kuwa damuwarsa ya samu kuɗin da zai canja waya, wani kuma damuwarsa ya tara kuɗin da zai yi aure, wata kuma damuwarta mamanta da babanta sun mutu a haɗarin mota yanzu an bar ta ita kaɗai ba ta da kowa, da dai sauransu. 


Ire-iren waɗancan misalai dake sama idan aka dube su da idon basira za a ga cewa sun faɗa ne a ƙarƙashin rukunai guda biyu wanda su ne musabbabi kuma dalilin samuwarsu. Waɗannan rukunai su ne; "Buƙatuwa" da kuma "Ɗimuwa" . Idan muka warware ta hanyar bayani zamu ga cewa, mai son tara kayan aure, mai son samo abin da za a ci a gidansa, da mai son canza wayar hanunsa daga karama zuwa babba da ma wanda burinsa daukar fansar wani abu da aka aikata masa ne dasauransu waɗannan duk suna cikin damuwa ce ta buƙatuwar da zukatansu ta kasance wajen ganin sun samu wani abu ko wajen ganin sun cimma wani ƙuduri na ran su ma'ana suna ɗauke da damuwa ce wadda ta ta'allaƙa ga samun biyan buƙatar rai. Shi kuwa misali na ƙarshe na nuni ne da damuwa irinta ɗimuwa wadda ta samu a sakamakon taraddadi na tunanin rashin madafa dake cuɗanye da alhini ko jimami na rashin wani da ake ga makusanci ne koma shi ne rayuwar ta dogara a kansa. 


Bakiɗaya kuwa, waɗannan damuwowi ne na halitta, ma'ana kamar yadda ake samun mutum da hanu, ƙafa, ido dasauransu a matsayin sashe na halittar jikinsa kwatankwacin haka su ma waɗannan nau'i na damuwowi suka kasance ga rayuwar Ɗan Adam domin suna da alaƙa da samuwar ɓacin rai da kumu ƙoƙarin cika buri shi wannan rashin sukunin da ake samu kafin burin ya cika shi ne Damuwar shi ne kuma irin damuwar da muka sani sannan kuma dukkaninsu nan take suke gushewa a neme su a rasa da sannu a hankali a cikin wani ɗan ƙanƙanin lokaci. Bambancin dake tsakanin biyun (Buƙatuwa da damuwa ta ɗimuwa) kawai shi ne "Damuwa ta bukatuwa" tana gushewa ne da sauri kamar harbawar kibiya misali wanda ke fafatukar samun abinci da zaran ya samu to shikenan ƙarshen damuwarsa kan wannan ya kau, haka wanda yake son sayen waya da zarar ya saya damuwarsa akan wannan ta ƙare. Ita damuwa ta ɗimuwa ita ce wadda akan ɗan ɗauki wani wa'adi a na cikinta misali wanda ke cikin damuwa ta jimamin mutuwar wani makusanci nasa yana iya ɗaukar kwanaki ko makonni kafin damuwarsa ta washe. Kun ga kenan idan muka taƙaita ta hanyar yin duba kan waɗannan misalai kawai da makaman tasu, muna iya cewa babu wani daban da ba shi da irin waɗannan damuwowin shiyasa ma kiran sunan damuwa bai zama wani abin ɗagun hankali ga ɗaukacin mu ba. Sannan idan muka taƙaita bayanin a jimla ɗaya muna iya cewa damuwa ita ce rashin sukuni a rai wanda ke haifar da rashin daɗin zuciya Sai dai abin tambayar a nan shi ne, shin irin waɗannan damuwowin da muke faɗawa ɗin ne muke jin masana kiwon lafiya na kiranta da suna "Depression"? amsar ita ce, a'a. 


To me ake nufi to da Depression?

A zahirin gaskiya, kalmar Depression a Hausa ta ma zarce mu ambace da suna damuwa kawai domin ita din ba ma wai lalura ba ce kawai, CUTA ce wadda abin da take shi ne ƙoƙarin tarnaƙi ga kyawoyin halittar da su ne maɗaukai na saƙonnin dake aikuwa zuwa ƙwaƙwalwar Ɗan Adam da ma sauran sassan jikinsa (Neurons). Inda a sakamakon wannan dabaibayi da tarnaƙin da su waɗannan maɗaukan sakonnin ke tsintar kansu a ciki ne, hakan ke jirkitar da aikinsu na aikawa ƙwaƙwalwa da kuma gangar jiki saƙo wanda kuma kan shafi lafiyayyen tunani gami da wanzar da samuwar ɗaci a zuciya wato ƙunci wadda hakan ke nufin zuciya kan tsinci kanta cikin matsanciyar damuwa ko damuwa mai tsanani. Kenan a nan ita kalmar "Damuwa" da ake fassara DEPRESSION da ita, alama ce daga alamomi bayyanannu da ake iya gane mutum ya kamu da cutar depression.


Bisa wannan ɗan gajeren bayanin wanda fassara ce na yi daga bayanin masana kiwon lafiya da kuma hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO), kai tsaye muna iya cewa Depression cuta ce dake sa girgizawar tunani (ba hauka ko gushewar hankali ba) wadda take samuwa yayin da maɗaukan dake tura sakonni a kwakwalwa (Neurons) suka shiga halin tarnaƙi da dabaibayi a sakamakon tsanantuwar ƙunci (wato damuwa).


Insha Allah, a rubutu na gaba zamu yi kokarin ƙara fayyace bayanin dalla-dalla tare da misalai masu yawa har ma kuma mu yi duba kan ire-iren cututtukan Depression, alamominsu da kuma yadda za ka gane shin ka kamu da cutar Depression ko kuma ba ka da ita da kuma hanyoyin da ake rabuwa da ita kai har da ma duba yiwuwar shin likitocin mahaukata suna iya gane mai cutar depression ko a'a.

Reactions
Close Menu