'Potiskum Writers' ta karɓi baƙuncin sabin marubuta

Safiyar jiya Asabar rana ce da ta zo daidai da lokutan da kungiyar Potiskum Writers Association (POWA) take gudanar da tarukanta na Dandalin Marubuta inda membobin kungiyar ke baje kolin fasaharsu a fannoni daban-daban da suka hada da kagaggun labarai, rubutattun wakoki, labarun ban dariya da barkwanci, rubuce-rubucen addini da ma wasannin kwaikwayo da sauransu.

Jerin marubutan da suka halarci taron baje kolin fasaha na POWA 


Taron wanda ya gudana a makarantar koyar da sana'o'i dake kwaryar garin Potiskum na jihar Yobe ya samu halartar sabbin marubuta masu tasowa da suka hada da Ahmed Nuhu, Suleiman Mahir, Abubakar Haruna Mu'azu, Adamu Aliyu Adamu, da kuma Muhammd Umar M.


Yayin gabatar da taron wanda kamar kullum shugaban kungiyar Musaddam Idriss Musa ya jagoranta, an gabatar da labarai da kuma rubutattun wakoki daga membobin kungiyar da suka hada da Mu'azu Dahiru wanda ya gabatar wakensa mai suna Duniyar Zamani, Mohammed Yusuf Ali (Ahasam) wanda ya gabatar da labarinsa mai suna Makarantar Gasa, akwai kuma Ibrahim Auwal Abubakar da ya gabatar da wake mai taken Mugun Bawa sai kuma a karshe Ali Dahiru El-Adi wanda ya gabatar da labarinsa mai suna Jatau Dan Maguzawa.

Reactions
Close Menu