RANAR 'YANCIN KASA
Anya ko zan murna da ranar'yantuwa *
Bayan kasata na ta ihun dimuwa?
'Yanci fa in har ba tsaro kuma ga tulin *
Yunwa fa bauta ne ga bautar bautuwa
Ya BABA ka san ni fa mai kaunarka ne *
Sakonka ga shi ka karkade masa kunnuwa
Ya Baba in har jar miyar ta gagara *
Kukar a saita ta da babbar daddawa
In ko da hali har da kifi dan kadan *
Dan galmi-galmi muke bida ko ba yawa
'Yar Gwamnatin in tai wuya to tamu fa *
Tai yo bagas mana kar ta sanya majaujawa
Ni tausayin Cil'a nake yai yekuwar *
Kawo dafa-duka an zugum ba amsuwa
Ya Baba ka san duk kasa an sallama *
Mai gaskiya kai ne fa me ke faruwa?
Ya Baba ka san 'yan arewa a kanka fa *
An kwashi kwarbai an ka fada damuwa
Dukkan musulmi kai wakili namu ne *
Sai sa nikabi in ka kasa farantuwa
In har ka kasa mun ji kunya har butur *
Wa zan amincewa a wannan rayuwa?
Na Ayagi ni dai na isar kuma na fita *
Sakonku kenan 'yan kasa ran 'yantuwa
Binyamin Zakari
(Abul-warakat Ayagi)
07082460196
30-9-2020
0 Comments