Yadda jarumai a Kannywood suka yi murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kan Najeriya

 Shekaran jiya Alhamis rana ce da Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai inda hakan ya sanya al'ummar kasar daga ko'ina a fadin duniya suka yi ta aikata abubuwan da suka hada da shafe jiki da fenti mai nuna alamar tutar kasar da launikan kore, fari a tsakiya da kuma kore, wasu kuma kan dinka suturu masu wannan launi, yayin da wasun kan yiwa gashin kansu ado duk dai da wannan launi ko ma dai daukar tutar kasar suna daga ta sama cike da farinciki duk don nuna murna da zagoyowar ranar samun 'yancin kai na kasar.Jaruma Maryam Yahaya


A bangaren jarumai da mawakan masana'antar shirya finafinam Hausa ta kasar, taurarin sun nuna nau'ikan nasu farincikin da ire-iren wadannan shiga inda suka yi ta dorawa a shafukansu na sada zumunta kamar su Instagram da kuma Facebook.


Ga dai hotunan wasu daga jaruman masana'antar da ke nuna irin shigar da suka yi don nuna murnar da zagoyarwar ranar ta samun 'yanci.Reactions
Close Menu