Yadda mata marubutan Hausa suka ƙwaci kan su daƙyar

Marubuciya Lantana Ja'afar 

A safiyar yau Asabar ne aka bayyana sakamakon gasar Gusau Institute a jihar Kaduna wadda ta dauki tsawon shekaru uku zuwa huda da fara gudanar da ita. Sai dai kuma tun bayan fara ita wannan gasa wadda kowane marubuci yake aika labarin da kalmominsa suka isa samar da littafi sukutum, ba a taba samun macen da ta taba zuwa ko da mataki na uku ba wanda dalilin hakan yasa marubuta maza da dama ke yiwa gasar kirari da kuma take iri daban daban da suka hada da "gagara mata" don zolayar takwarorinsu mata da ake yiwa kallon sun gaza a gasar.

Marubuciya Zulaihat Sani Kagara


Sai dai kuma sakamakon gasar na bana ya zo da dumbin al'ajabi tare da bude sabon babi a tarihin gasar wadda ake yiwa kallon marubuta maza ne suka yiwa babakere tare da ture takwarorinsu matan a gefe inda a sakamakon na bana alkalan gasar suka bayyana tagwayen marubuta mata Zulaihat Sani Kagara a matsayi na ta uku da kuma Lantana Ja'afar a matsayi na ta biyu inda kuma gwarzon gasar ya kasance namiji wato Jibrin Adam Jibrin wanda ya zo na daya.
Kenan a na iya cewa, marubuta mata a bana sun kwaci kansu dakyar tare da sake tabbatarwa da kuma nunawa takwarorinsu mazan cewa, "dama can kyale ku muka yi".Lantana Jaafar, Jibrin Adam tare da Zulaihat Kagara

Reactions
Close Menu