Alan Waka, Gidan Dabino, Dorayi da sauran taurari sun samu kambun gwarzantaka na 2020

Daga hagu Hajiya Balaraba Ramat, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, Haj. Bilkisu Yusuf Ali tare da sauran mahalarta taron.

A makon da ya gabata jerin wasu jajirjattu kuma shahararrun taurari a masana'antar Kannywood da suke taka rawa a bangarori mabambanta cikin al'amuran tafiyar da harkokin na fim suka samu kambu na lambobin yabo a yayin bikin C-MAP na bana mai taken "Night of Fame". 


Daga manyan taurarin da aka karrama din akwai fitaccen marubuci kuma dan wasan kwaikwayon gidan talabijin na Arewa24, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, da sanannen mawaki Alhaji (Dr.) Aminu Ladan Abubakar, da kuma shaharren darakta, marubuci kuma dan wasan barkwanci Malam Falalu Dorayi. Akwai kuma tsohon mawaki Mudassir Kasim da kuma masharurin marubucin labarai da wasannin kwaikwayon nan Malam Nazir Adam Salihi. C-MAP ta karrama su ne bisa rawar da kowannen su ya taka a bangaren da yake da kwarewa akai bayan ta waiwayi ayyukan masana'antar nishadin daga watan farkon wannan shekara zuwa yanzu wanda hakan yasa ta zabe su a matsayin gwarazanta na wannan shekara.


Daga manyan bakin da suka halarci taron akwai wasu daga shahararrun marubuta mata da suka hada da Hajiya Balaraba Ramat da kuma Hajiya Bilkisu Yusuf Ali.

Reactions
Close Menu