An buɗe gasar gajerun labarai mai taken "Siyasa 'yanci"

Biyo bayan sa hanu kan wata sanarwar da ta fita a daren jiya Alhamis, kungiyar marubuta na Potiskum Writers Association da ake kira POWA ta fidda sabon tsarin gasarta na watan Nuwamban da muke ciki inda a wannan karon ta samar da take a maimakon jigo kamar yadda ta saba gudanarwa a kowanne karshen wata. Taken gasar dai a wannan karon shi ne "Siyasa 'yanci" ga kuma yadda kungiyar ta bada sanarwar tsarin yadda gasar za ta gudana:

Tsarin gasa:

1. A na so kowa ya yi rubutu cikin nuna kwarewa tare amfani da salo mai jan hankali wajen fidda wani batu (jigo) da kai tsaye ke da alaka da siyasa. Rubutun zai iya zama kan matsolin da siyasa ke haifarwa ko cigaban da siyasa ke samarwa da sauransu.

2. Gajeren labari, wasan kwaikwayo ko rubutacciyar waka ne kawai za a iya shiga gasar da su.

Kwamitin alƙalai sun bayyana marubuta shiga da suka yi nasara a gasar gajerun labaran powa

3. Duk rubutun da aka shigar dole ya kasance mallakin wanda ya shiga gasar ne kuma ba a taba buga shi a wani wurin ba a baya. Sannan dole mai shi ya tabbatar da cewa idan yayi nasara zai killace labarin ba zai fitar da shi ko shiga wata gasar ta daban da shi ba har sai bayan an wallafa kundin gajerun labaran POWA a cikin watan Janairun shekara mai zuwa.


4. Rubutun dole ya kasance a daya daga cikin wadannan harsunan (Hausa/Turanci)


5. Gajerun labarai dole yawan kalmomin su kai 1000 kuma kar su wuce 1500.


6. Rubutacciyar waka dole ta kai baituka 20 kuma kar ta wuce baiti 50.


7. Dukkan labaran dole su kasance an yi kokarin bin ka'idojin rubutu.


8. Da labari daya kowane mutum zai shiga gasar.


9. Za a tura labarin shiga gasar ta WhatsApp a wannan lambar +2349063064582 ko kuma a +2347067132948.


9. Wadanda labaransu suka tsallake tantancewar da jami'in gasar yayi, za a bukaci su tura labaran zuwa ga alkalan gasar ta adireshin email na kungiyar.


10. Bayan tattara labaran za a buga sunayen wadanda suka shiga gasar a shafuka da kuma zaurukan kungiyar.Ranar rufe shiga gasa: 22 ga Nuwamban 2020, da misalin karfe 5:00 na yamma. Lokacin karbar gasar zai fara daga karfe 5:00 na yammacin yau Juma'a.Za a fadi sakamakon a ranar/kafin ranar 1 ga Disamban 2020.Allah ya bada sa'a. Amin


Reactions
Close Menu