An taba min marin da sai da na ga wuta - in ji Shehu Hassan Kano

Malam Shehu Hassan Kano


Malam Shehu Hassan Kano wanda daya ne daga dattijan da suka dade a ganinsu a akwatinan talabijin suna taka rawa a matsayin jaruman shirin wasan kwaikwayo a masana'antar shirya fina-finan da a yanzu ake wa lakabi da Kannywood ya bayyana cewa wani mari da aka taba yi masa a da can baya wanda yayi sanadiyar da sai da ya ga tartsatsin wuta a idonsa na daga jerin abubuwan da ba zai taba mantawa da su ba.


Malam Shehu Hassan din dai ya bayyana hakan ne biyo bayan sallamo shi daga asibiti bisa aikin ido da aka yi masa a tattaunawar da aka yi da shi cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na BBC inda ya bada labarin afkuwar lamarin da cewa,


Watarana ne mun je kallon wasan duma sai na kalli wani Bagobiri yayi kwal-kwal ya shafa mai kan yana kyalli, ni kuma kawai ba abin da ya ban sha'awa in ban da na daki kan wannan bagobirin... In ji Malam Shehu Hassan Kano.


Inda kuma ya cigaba da bada labarin yadda lamarin ya faru da cewa, 

To na zo kawai a na rawa, a na rawa kawai da ta dauke sai na dube shi tas! Na daki kan wannan Bagobirin. Wannan dukan da nayi masa da ya waigo kuwa ya tashi yayi min barin makauniya ni da kaina na sa ihu nake cewa abokaina a kashe mita a kashe mita, na dauka tartsatin wuta ne ake yi saboda irin abubuwan da na gani fafar-fafar a idona sai na ji a na ta dariya a she dai bagobiri ne ya mare ni to shi wannan marin ba zan taba mantawa ba.


Da aka tambaye shi ko yana rera waka, Malam Shehu Hassan din dariya yayi tare da cewa, 

Ni ina zaton idan nace zan yi waka gaskiya duka za a yi min saboda muryata ba ta mawaka ba ce.

 A cewarsa.


Daga karshe Malam Shehu Hassan din ya bayyana ganin samari sun zama mutanen kirki a matsayin babban abin da yafi faranta masa rai.

Reactions
Close Menu