Bayan Irrfan, daya daga jarumai masu lakabin "Khan" ya sake mutuwa

Yayin da 'yan kallo ke cike da buri na son cigaba da kallon fuskokin jaruman su bayan dawowar masana'antar Bollywood daga dakatar da ayyukanta da hukuma tayi saboda halin barkewar cutar nan ta annobar korona ake cike, mafarkin wasu dubban masoya finafinan Bollywood din na son sake ganin fuskokin jaruman da suke so a jerin sabbin fina-finai ba zai cika ba sakamakon yankan kaunar da mutuwa ta yi a tsakaninsu da taurarin nasu.

Hoton wasu musulmai a yayin da suke binne gawa a kasar Indiya

Idan ba a manta ba a watanni kadan da suka wuce baya, Mujallar ADABI ta samar da rahotanni kan mace-macen wasu shahararrun jaruman fim da suka riga mu gidan gaskiya a masana'antar wanda daga cikinsu harda sanannen jarumin nan kuma daya daga taurarin Bollywood musulmai dake taka rawa a masana'antar mai suna Irrfan Khan.


Wata sanarwa da ta fito daga shafin Pooja Batt, jaruma kuma mai shirya fina-finai a masana'antar Bollywood a shekaran jiya Laraba na dauke da sakon dake bayyana cewa a ranar Allah ya karbi ran fitaccen jarumin nan Faraaz Khan wanda daya ne daga 'ya'yan tsohon jarumi Yousouf Khan ya mutu a sakamakon harbuwa da cutar kansar kwakwalwa.


(Hagu) Marigayi jarumi Faraaz Khan, jarumi Farhaam Khan kaninsa


Sakon Pooja din dai ya zo ne a siga kamar haka: “Cike da jimami ainun nake mai bayyana labarin cewa #FaraazKhan ya tafi ya bar mu izuwa wajen da nake da nayi imanin yafi nan. Godiya ga dukkanin taimako da sakonnin fatan samun sauki da kuka yi masa a yayin da yake tsananin bukatar hakan. Ina rokon da ku cigaba da tuna iyalansa tare da sanya su a cikin addu'o'inku". In ji Pooja.


Jarumi Faraaz din dai ya mutu ne yana da akalla shekaru 50 a duniya kamar yadda jaridar Guardian da kuma Gulf suka ruwaito. 


Faraaz Khan


Kafin mutuwar Faraaz din dai an kwantar da shi a asibitin Mumbai kan matsalar cutar dake da alaka da kirji inda har a watan da ya gabata kaninsa jarumi Farhaam Khan ya bude asusun neman tallafi don biyan kudin aikin da za a yi masa wanda kuma nan take jarumi Salman Khan ya bayyana cewa zai biya kudin maganin.


Daga jerin finafinan marigayi Faraaz Khan din dai akwai Mehndi (1998), Fareb (1996), Dulhan Banoo Main Teri (1999) da kuma Chand Bujh Gaya (2005).

Reactions
Close Menu