BINTU 'YAR FULANI


Kyau ina kake ga gabanka,

Ka ajje duk jiji da kanka,

Sarauniyar ka take kiranka,

Wacce a kyau ta zarce kowa.


In ma'anar so ne fa kyawu,

Tun daga kai ka haɗa da sawu,

Babu ya Bintu ɗiya ta Kawu,

Kallonta ke sa ni murmusawa.


In za a sa a caken da Mashi,

Muddin idonta ina ganin shi,

Zafi ba zan ji ba don shigar shi,

Ballantana a ji nayi ƙuwwa.


Jinin uwa ahali na Fillo,

Ke zan biyawa kuɗi na lilo,

Wanda ya kalleki za na wullo,

Sanda a kai nasa ba tsayawa.


Mai kyan hali ga yawa na kirki,

Ko a rugar mu kuna da mulki,

Ko an kiran bawa gare ki,

Batun ga sam ni ban kulawa.


Kira guda ki riƙe amana,

Ba ni da shanu ban da gona,

Amma akwai rumbu na ƙauna,

Da acciki za ki watayawa.


© Waƙar: Musaddam Idriss Musa

Reactions
Close Menu