Ɗaukacin daraktoci da masu harkar fim sun yi taron gangami wajen kallon shirin 'Tauraron Ɓoye'

Shu'aibu Lilisco (daga hagu), Sani T.Y Shaba (a tsakiya) tare da darakta Kamal S. Alkali a yayin haska fim din Tauraron Boye

Daga karshen makon da ya gabata kawo yanzu lokaci ne da ake cigaba da haska shirin T. Y Shaba mai suna 'Tauraron Boye' a film house cinema dake shoprite a birnin Kano.

Jaruma Samira Ahmad (ta biyu daga hagu) tare tsohon mijinta T.Y Shaba da sauran taurarin da suka je kallon shirin Tauraron Boye


Fim din wanda wasu ke ganin cewa ya zo da wani sabon salo irin wanda ba a saba ganin irinsa ba a cikin masana'antar ta Kannywood ya samu karbuwa tare da daukar hankalin jama'a 'yan kallo har ma da masu ruwa da tsaki a al' amuran shirya  fina-finai na masana'antar ta Kannywood.

Mawaki Oshere (daga dama) tare da Nomiss Gee a wajen kallon shirin Tauraron Boye


Da yake hira da manema labarai a kan nau'in sakon da shirin ke dauke da shi,  T Y Shaba ya bayyana cewa,

Fim din Tauraron boye yana nuni ne da irin yadda yara masu kwazo su ke tasowa da basirar su da kwarewa yadda jama'a za su amfana, to Amma sai ka ga iyaye sun dora su a kan wani ra'ayi na su wanda bai yi dai-dai da baiwar da suke da ita ba, sai ka ga ana yin kokarin a dora yara a kan wata kwarewa ko wani tafarkin da kwakwalwar yaron ba za ta iya dauka ba, daga karshe kuma za a iya samun sabani daga wajen yaron ko kuma a samu matsaloli wajen aikin da aka ce sai ya koya, don haka muka tsara labarin a kan wannan...

Samira Ahmad, mahaifiyar Sani TY Shaban wanda ya fito a matsayin Tauraro a cikin shirin


Fim din dai ya kunshi jarumai da dama na cikin masana'antar finafinai ta Kannywood da kuma takwararta dake kudanci wato Nollywood. Kuma an samo dandazon mahalarta da tururuwar jarumai da suka halarci gidan siniman inda suka kalli fim din tare da jaruman cikin shirin.

Reactions
Close Menu