Indiyawa sun shigar da karar Amitabh Bachchan a Kotu

 “Wane littafi mai tsarki ne Dr. BR Ambedkar tare da mabiyansa suka kona a ranar 25 ga watan Disamban 1927?”

Jarumin Bollywood, Amitabh Bachchan


Shahararren tauraron fim din nan na Bollywood dake kasar Indiya Amitabh Bachchan wanda ya kasance mahaifi ga jarumi Abisheik Bachchan kuma suruki ga jarumar da ta kasance tsohuwar sarauniyar kyau ta duniya, Ashwarya Rai Bachchan ya samu sammacin kotu biyo bayan shigar da kararsa da wasu fusatattu daga 'yan kasar ta Indiya masu kishin al'ada kuma mabiya addinin Hindu suka yi bisa abin da suka kira da "yin izgilanci ga addininsu".


Hauhawar al'amarin wadda ta samo asali daga masu amfani da kafafen sada zumunta na yanar-gizo tun a shekaran jiya Talata ya fusata Indiyawa da dama inda nan take suka shiga kamfen din nuna kin jini ga tashar da jarumi Amitabh Bachchan din yake gabatar da shirin kacici-kacicin da ya zamo silar barkewar matsalar da har ta kai 'yan kasar suka maka shi a kotu.

Bangon littafin addinin Hindu, Manusmirti


Jarumi Amitabh Bachchan, din dai shi ne wanda yake daukar nauyin wani shirin gidan talabijin a kasar da ake kira da suna 'Kaun Banega Crorepati' kuma matsalar ta danno kai ne biyo bayan wata tambaya da shi Bachchan din ya gabatar a cikin zangon "Karamveer" wadda ke da alaka da wani tsohon littafin addinin Hindu da ake kira da suna "Manusmirti" inda kuma wadanda suka kasance bakinsa a wannan zango suka kasance jarumin Bollywood Anoop Soni da kuma Bezwada Wilson wanda ya kasance dan fafutuka ne a kasar ta Indiya.


Tambayar wadda duk wanda ya ba amsarta zai samu Rs 640,000 wato kimanin N3,200,000 na kudin Najeriya ta kasance ne kamar haka,

 Wane littafi mai tsarki ne Dr. BR Ambedkar tare da mabiyansa suka kona a ranar 25 ga watan Disamban 1927?

Jerin amsoshin kuma sun kasance ne kamar haka

 a) Vishnu Purana, b) Bhagavad Gita, c) Rigdev, and d) Manusmriti.” inda kuma amsar ita ce Manusmriti.


Jarumi Amitabh Bachchan


Karin hasken da jarumi Bachchan din yayi akan amsar da cewa, a shekarar 1927, Ambedkar ya karyata ingancin littafi mai tsarkin da mabiya addinin Hindu din ke bi din ne mai suna Manusmriti wanda har ta kai shi ga kona kwafi da dama na littafin shi ne abin da ya janyo fusatar Indiyawan inda suka danganta hakan a matsayin wata hanyar neman kaiwa ga cimma wata manufa ta yada farfaganda game da addinin.

Reactions
Close Menu