Jarumin fim a Kannywood yayi wa Gwamnan jahar Yobe takwara

Shahararren dan wasan Kannywood din nan da ya dade a na damawa da shi a fannin fina-finan barkwanci na masana'ar Kannywood da ake kiransu da suna 'yan camama, Alhaji Mato Yakubu wanda a baya aka fi sani da Nakunduba wato Malam Nata'alan shirin dadin Kowa na tashar arewa24 yayi wa Gwamnan jihar Yobe dake kan gadon mulki wato mai girma Honarabul Mai Mala Buni mai suna a makon da ya gabata.

Hoton jaririn da aka radawa sunan Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni 

Addu'ar sunan wadda ta gudana a ranar Larabar da ta gabata a kofar gidan jarumin dake garin Potiskum na jihar Yobe, ya samu halartar dandazon jama'a wadanda suka je don taya shi murna.

Malam Nata'ala rike da jaririn da ya yiwa Gwamnan Yobe mai suna


Malam Nata'alan dai shi ne ke rike da sarautar sarkin barkwancin fadar Fika kuma shi ne ke rike da mukamin mai ba wa Gwamna Mai Mala Buni shawara ta musamman a bangaren kafafen sada zumunta. Mujallar ADABI na taya Malam Na ta'ala murna tare da fatan Allah ya raya Mai Mala Buni karami.

Reactions
Close Menu