"Ka tabbatar da sahihancin labari kafin ka yada shi da baki ko social media" - in ji Falalu A. Dorayi

Shaharrarren mai bada umarnin fim a masana'antar Kannywood din nan kuma mashiryin fina-finai, marubucin fim kana dan wasan Hausa take taka rawa a matsayin jarumi Falalu A. Dorayi mazauni a birnin Kano ya yi jan hankali ga masu yada labaran karya da cewa yi hakan yana haddasa fitina, gaba, kiyayya da rashin kwanciyar hankali tsakanin Al'umma.

Hoton Falalu A. Dorayin cikin shirin Kwana Casa'in na Arewa24


Tauraron wasan kwaikwayon wanda a yanzu haka fuskarsa ta mamaye gidajen al'umma bisa kallon sa da a ke a kwatinan talabijin cikin shirye-shirye masu dogon zango na tashar arewa24 da suka hada da shirin Gidan Badamasi da kuma Kwana Casa'in ya bayyana hakan ne a yau Juma'a cikin wani rubutu da ya saka mai taken "Labaran Karya" inda yake cewa,

Labaran karya da Jita-Jita dabi'a ce da ta zamo ruwan dare cikin mutane, lallai ne musulmi ya nisanci yada Jita-Jita da labaran karya, zancen da baka da tabbas ya faru amma ka bada labarinsa...

 In ji darakta kuma dan wasan Falalu A. DorayiA cikin rubutun nasa dai har wayau, jarumin ya ci gaba da jan hankalin al'umma ta hanyar tsoratar da su illar yada labaran kanzon kuragen da cewa,

An ba mu labarin DUJJALAWA a karshen zamani, zasu dinga tsara Jita-Jita har sai wadansu mutane sun ringa daukar jita-jitarsu kamar fadar Alkur'ani


Ya kuma dora da bayanin yadda masu yada jita-jita suke kawo hargitsi da rusa zaman lafiyar dake tsakanin al'umma da kuma yadda hakan zai zamo matsala ga masu yi idan suka mutu akan wannan turba ta yada labaran karya inda yake cewa,

Sharrin Jita-Jita da labaran karya suna haddasa fitina, gaba, kiyayya da rashin kwanciyar hankali tsakanin Al'umma. Sannan za ta zamo TOZARTA ga wadanda suke yinta ranar ALKIYAMA.Jan hankalin da jarumin yayi bai tsaya iya nan ba sai da ya kawo fadin Allah madaukakin Sarki kan masu aikata wannan barna kamar yadda ya rubuta cewa,


"UBANGIJI (SWT) Yace;

Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game dashi. Lallai ne Ji da gani da zuciya, dukan wadancan(mutum) ya kasance daga gareshi wanda ake tambaya.

 Da kuma inda UBANGIJI (SWT) Yace;

Ya ku wadanda suka yi Imani! Idan fasiki ya zo muku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuma masu nadama. 

Daga karshe jarumin ya rufe nasihar tasa da cewa,

Ga mai hankali sai ya kiyaye irin labaran da zai ringa dorarwa ga mutane, musamman a wannan lokacin da karyar tafi yawa a Labaran da muke karantawa...Dukkan abin da bawa zai fadi ka tabbatar da sahihancin labari kafin ka yada shi da baki ko social media....Allah ka tsare mana harshen mu.

Reactions
Close Menu