Rayaas: Saƙon taya murna ga Malam Muhammad Umar Gombe

Bayan godiya ga Allah madaukakin sarki, ina farin cikin sanar da 'yan uwa da abokanen arziki musamman membobi da shugabannin kungiyar RAYAAS, Malam  Umar Mohammad Gombe (National Coodinator) ya zama Editan Jaridar Blueprint MANHAJA, mallakar Kamfanin Jaridar BLUEPRINT NEWSPAPERS MEDIA LIMITED, wacce zata riqa fitowa duk ranar Juma'a

Hakika wannan abin farin cikine kuma babban ci gabane ga wannan kungiya da membobinta baki daya, muna taya shi murna da fatan Allah madaukakin sarki ya tayashi riko bisa gaskiya da rikon amana. Sannan ya hada shi da abokanen aiki na gari masu kishin kasa da cigaban al'umma.


Bayan haka ina muku albishir na musamman da cewa an warewa kungiyar RAYAAS katafaren shafi da zai rika zagawa jahohi tare da kawo rahotonnin aiyukan alkairi da muke gudanarwa a birni da karkara. Don haka ina amfani da wannan dama wajen kira ga shugabannin jahohi su kara himma wajen gudanar da sabbin aikace-aikacen kungiya kamar yadda su ka saba. Sannan kuma su rika aika cikakkun rahotannin abubuwan da su ka aiwatar duk mako domin raya wannan shafi da aka bamu. Kamar yadda na rubuta a sama jaridar za ta rika fitowa ne duk ranar Juma'a a kowane mako, in sha Allahu daga wannan juma'ar za'a fara samunta a kasuwanni da guraren sayar da jaridu a fadin tarayyar kasarnan, wani abin farin ciki shafin kungiyar RAYAAS na daga cikin shafukan farko da aka fara yiwa jaridar MANHAJA sharar fage da su a rubuce.Muna godiya Malam Umar, da fatan Allah ya kara daukaka da basira.


Daga: Auwali Adamu Differences Sakataren Tsare-Tsare Na Kasa Baki Daya.

Reactions
Close Menu