Ruɗun Zamani rubutaccen waƙe ne da Musaddam Idriss Musa suka rubuta a matsayin waƙar haɗin gwiwa shi da Zahra SQ a watan Nuwamban shekarar 2020
Sunan waƙa: RUƊUN ZAMANI
*Zahra:*
Bismika Sarki Gwani
Tabara yo mana lamuni
Mu waƙe wannan zamani
Dake tsaka na hatsaniya.
*Musaddam:*
Yau duniya ta birkice
Ga al'umma sun haukace
Duk hankali nasu ya ɓace
A gurin biyewa zuciya.
*Zahra:*
Mun biyewa so na rai
Wanda ke janyowa kai
Tsangwama har ma a kai
Mu zamma tamkar mujiya
*Musaddam:*
'Yan uwa mun kaurace
Gun mu sun zama tarkace
Ba zumunci ya mace
Mun kauce hanyar anbiya
*Zahra:*
Ba maza yau ba mace
Gulma har da su yafice
Ba guda wanda za a ce
Ya ci a yi masa kariya.
*Musaddam:*
Ya kamata kwarai a yau
Ayyukan kirki mu hau
John, Madina, Ari, Barau
Kafin barin mu na duniya.
*Zahra:*
Rabbi mai ji mai gani
Wanga ruɗun zamani
Dake ta bin mu dare, wuni
Sa muke ta yi masa turjiya.
0 Comments