'Masana'antar Bollywood kamar Kura ce da fatar Akuya' in ji Jarumi Emraan Hashmi 

Emraan Hashmi


A daidai lokacin da ake shirin sake sabin finafinansa da suka haɗa da 'Chehre' da kuma 'Mumbai Saga' jarumin masana'antar Bollywood ɗin wadda ke ƙasar Indiya Emraan Hashmi ya bayyana masana'antar da cewa "jebu" ce. 

Sauke Manhajar Mujallar ADABI Kan Wayarka a Yau Ta Hanyar Taba Wannan Rubutun 

EmraanHashmi dai ya fara tashe ne tun bayan fitowar fim ɗin Raaz da ake sake a shekarar 2002 wanda hakan ke nuna cewa zuwa yanzu jarumin ya shafe kusan shekaru 20 a masana'antar ta Bollywood. 


A yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai, jarumin ya bayyana mamakinsa kan yadda ya tarar da komai na masana'antar saɓanin yadda ake faɗarta. 

Download Mujallar ADABI application on your android phone today

A cewar Emraan ɗin ya ja da baya ga sha'anin masana'antar ne saboda lura da yayi da cewa duk sakin fuskar nan da jaruman ke nunawa a fili ba shi ne abinda yake zamowa haƙiƙanin abinda ke zukatansu ba a zahiri. A cewarsa duk wannan na jabu ne kuma lamari ne irin wanda za a kira da 'Kura da fatar Tinkiya'. 


Sabon fim ɗin nasa na Chehre ɗin dai wanda Rumi Jaffrey ya bada umarni na ɗauke da manyan jarumai kamar Amitabh Bachchan wanda zai fito a matsayin lauya kuma a na sa ran sakin fim ɗin a gidajen sinima a watan Afirilun 2021.

Maza sauke Manhajar Mujallar ADABI a wayarka don samun labaran mu kai tsayeReactions
Close Menu