"Na yi nadamar rashin godewa Allah da na yi" - Bhagyashree

 "dukda na shafe sama da shekaru talatin rabon da na fito a fim har yanzu a na tuna suna na....."

Hoton Jarumar Bollywood Bhagyashree


Ranar 23 na Fabairun da muke ciki ya kasance rana ce da shahararriyar jarumar finafinai na ƙasar India dake aiki da masana'antar Bollywood wato jaruma Bhagyashree tayi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta wanda hakan yasa dubbanin masoya tare da abokan aikinta suka tayata murna. 

Taba wannan shudin rubutun don sauke manhajarmu

    Sai dai furucin da jarumar tayi kamar yadda jaridar Hisduntan Times ta ruwaito na nuni da cewa jarumar tayi bikin murnar haihuwarta ta ne a bana cike da nadamar wasa da damarta da tayi wadda ta samu cikin masana'antar tun lokacin fim ɗinta mai suna 'Maine Pyaar Kiya' wanda tayi shi tare da shahararren jarumin Bollywood ɗin nan da ake yabo a matsayin mafi kyan ƙirar jiki na masana'antar wato Salman Khan. 


    Bhagyashree ɗin ta bayyana cewa, a yanzu da take da dama ta biyu tana so ne ta gyara kuskuren da ta yi a baya na rashin yabawa gami da kuma nuna hamdala bisa nasarar da ta risketa a cikin ƙanƙanin lokaci cikin sana'arta ta wadda ta gaza yin hakan a lokaci na farko wanda hakan yasa ta kasa kai ga cimma burinta. "Ban nuna godiya ba sam kuma ban daraja nasarar da na samu ɗin ba" in ji jaruma Bhagyashree a yayin hirarta da manema labarai. 


 Jarumai kan yi aiki tuƙuru don ganin sun kai ga taka matakin samun irin ita waccan nasarar da na samu a sauƙaƙe, kuma a cikin ƙanƙanin lokaci. Ina jin kamar ban kasance mai hamdala ba ga Ubangijina saboda ya ba ni ɗin kuma ban nuna godiya ta akan hakan ba. Sai dai a yanzu na ɗauki hakan a matsayin wani darasin rayuwa a gare ni.


Jarumar wadda a da ta watsar ta aikin nata na fitowa a finafinai ta rungumi aikin kula da iyalinta ne kawai a yanzu ta dawo cike da ƙwarin gwiwa gami da lasar takobi da cewa, 

"dukda na shafe sama da shekaru talatin rabon da na fito a fim har yanzu a na tuna suna na. Don haka wajibi ne a kaina na yi abinda ya kamata don nuna mafi girman godiyata bisa damar da ta zo min. Ina kuma fatan har yanzu 'yan kallo za su sake nuna min so da ƙauna. Da ina ilimin darasin da na koya a yanzu da babu yaddda za a yi na bar yin fim" in ji ta.

Za ku iya hira, aika mana rubuce-rubucenku, da kuma kafta muhawara da ma wasanni don nishadi. Sauke manhajar Mujallar ADABI ta hanyar taba wannan rubutun don shiga sahun masu kallon mu cul-da-cul


Reactions
Close Menu