‘An taɓa yin barazanar yi min fyaɗe saboda ina rubutun Hausa’ – in ji Rahma Ahmad

Rahma Ahmad (Gimbiya Rahma)

R

ahama Ahmad Wadda aka fi sani da Gimbiya Rahama matashiya ce ‘yar asalin jihar Kano kana kuma kwararriyar marubuciyar yanar-gizo. A tattaunawarta da wakilin Mujallar ADABI, Musaddam Idriss Musa, marubuciyar ta bayyana dalilan da suka kai ta ga fadawa harkar rubutu tare kuma da burin da take da shi game da rubutu a halin yanzu har ma da zuwa nan gaba. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

 

Zan so ki fadawa masu karatu tarihin rayuwarki a takaice, shin wace ce Gimbiya Rahama?

 

Da farko dai sunana Rahma Ahmad, an haife ni a garin kano cikin unguwar Gwale, Na yi dukkan karatuna daga Firamare har zuwa sakandire duk a nan. A yanzu haka dai ina zaman jiran adimishan ne.

 

Batun iyali fa, ban ji kin saka wannan a lissafi ba?

(Murmushi) a’a ba ni da aure sai dai niyya.

 

To Allah ya kawo abokin zama nagari. Shin ya aka yi kika tsinci kanki a fagen rubutu?

 

Na tsinci kaina a harkar rubutu ne saboda so da kauna da kuma sha’awa da nake yi na fadakarwa ga al umma.

 

Kawo yanzu tsawon wane lokaci kika dauka kina rubutu kuma adadin littattafanki za su kai nawa?

 

Littattafai na suna da yawa, amma a yanar-gizo guda biyar ne kawai kuma na fara rubutu ne sama da shekaru takwas baya amma a yanar-gizo ban fi shekara biyu ba da farawa a nan.

 

Mene ne sunan littafinki na farko kuma wane sako yake kunshe da shi?

 

Littafina na farko shi ne Kallon Kitse, yana isar da sako ne akan muzgunawar da wasu ‘yan uwan suke wa ‘yan uwansu har karshe ta kai su ga nadama.

 

Wane irin kalubale kika tsinci kanki a yayin da kika fara rubutu?

 

Rahma Ahmad (Gimbiya Rahma)

Bai wuce na jama’a ba…saboda ka san jama’a sai hakuri, da yawa idan ka yi rubutu wasu kan yi maka kallon banza shashasha marar aikin yi saboda mu muna tsarkake rubutunmu ba kamar masu bayyana batsa da rashin da'a a cikin nasu ba. Matsalar da na taba fuskanta ita ce da ake bina har inbox a zage ni, a kirani har da karuwa duk a silar rubutu. Ni har wani cewa yayi sai yasa an yi min fyade saboda wai tun da na fara rubutu nake ji da kaina.

 

Wadanne irin nasarori kika samu a fagen rubutu?

Nasarori kam alhamdulillah, domin ko a yanzu sai dai na godewa Allah akan rubutu na samu karramawa ta satifikit har guda uku.

 

Kasantuwarki matashiyar marubuciya kuma budurwa. Ya kike ganin rayuwar rubutun ki zata kasance bayan aurenki?

 

Ina fata hade da sa ran cigaba da rubutu har karshen rayuwata. Aure baya hana gudunar da abubuwan cikin rayuwa don haka ina sa ran aure ba zai taba hana ni rubutu ba.

 

An san marubuta da iya siffanta taurarin labaran su, zan so kiyi amfani da wannan salon wajen siffanta mana shin wane irin miji ne Gimbiya Rahama take son aura?

 

Uhmm. Mijina (dariya) wanda zai rika tausaya min dare rana, mai addini a kodayaushe. Haka kuma ya kasance dogo, fari ne ko baki wannan ba matsala, mai matsakaicin jiki, bana son lukuti kuma ya kasance dan gayu wanda ya iya kwalliya sai dai ba na son kyakkyawa saboda halin matan mu na yau.

 

Akwai wani tasiri ko sauyi da rubutu ya kawo a rayuwarki, mene ne?

 

Gimbiya Rahama: Gaskiya akwai. Domin rubutu yasa ina jin kaina ni wata ce wanda ada bana yi. Haka kuma rubutu yasa ina jin zan iya hira da kowa ciki har da shugaban kasa. Haka kuma rubutu ya sauya ni daga shiru-shiru zuwa mai surutu ga kuma ilimi da na sake samu duk a fagen rubutu.

 

Da za ayi miki kyautar N100,000 a matsayin tallafi gareki don bunkasa rubutunki ya za ki yi da kudin?

 

“Kai! a bani dubu dari a rayuwa dan bunkasa rubutuna kawai. Babban abu na farko shi ne zan buga littafi da ita sauran canjin kuma zan samu wata sana’ar data dace na yi don ganin ban zauna haka kurum ba.

 

A karshe wane sakon kike da shi zuwa ga masoyanki da kuma Mujallar ADABI?

 

Gimbiya Rahama: Sako na zuwa ga masoyana shi ne ku cigaba da sawa a ranku cewa har abada ba zan taba mantawa da ku ba domin kuwa kun min komai a rayuwa ina matukar alfahari da ku a duk inda kuke, ina kaunarku masoyana. Ina kuma mika sakon yabo da jinjina ga Mujallar Adabi, Allah ya cigaba da daukakaki har abada ku cigaba da nishadantar damu. Nagode.

Reactions
Close Menu