Arewa24: Tasiri Da Raunin Shirin Dadin Kowa Ta Fuskar Inganta Tsaron Kasa (1)

 

Babu mutumin da zai dubi shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24 yace shirin ya gaza musamman ta bangaren marubutan dake aikin rubuta shi. Kana kuma ko da ga wanda bai san su waye suke rubuta shirin ba kusan ina iya cewa babu bukatar tsayawa yin dogon bayanin cewa kwararru ne a fannin kuma masu ilimi kan yadda ake shirya rubutu misali mafi kusa shi ne kan irin karbuwar da shirin ya samu ga dubban mutane daga yankunan kasashe daban-daban na sassan da ake magana da harshen Hausa da kuma yadda aka kwashi tsawon lokaci ko ma nace shekaru a na haska shirin tun daga kan na farkon mai suna Dadin Kowa da kuma Sabon Salo izuwa kan wanda ake yanzu mai taken Wasa Farin Girki, ganin yadda dubbanin al’umma suke cigaba da bibiyar shirin ba tare da kosawa ko gimsa ba kadai ya isa ya tabbatar gami da gamsar da duk mai sha’awar son sanin marubutan shirin da cewa ba kananan gwaskaye ba ne kuma sun nakalci aikinsu yadda ya kamata.


Wani babban abin daukar hankali game da shirin Dadin Kowa wanda kusan a na ma iya cewa shi ne yake da rinjaye mafi tsoka daga jerin abubuwan da suka sa shirin ya kama zukatan mutane shi ne salon tafiyar sa da zamani wato yadda marubutan suke gina labarin shirin a yanayin dake kama kai-da-kai da halin da al’umma take ciki a rayuwar zahiri ta yadda kai dake kallo idan wani abin bai zo a sigar da yake daidai da rayuwarka ba, za ka tarar ya zo daidai da ta makocinka ko wani dan unguwarku. A takaice shirin ya zama kamar wani madubi ne da al’ummar mu take ganin kanta a ciki domin babu fannin da bai taba ba kama daga nuni kan irin rayuwa ta nakasassu masu yawon bara, irin zubin rayuwar talaka a kasashen Afirka masu tasowa kamar kasashen Najeriya da Nijar, rayuwar zamantakewar musulmi da kirista, dabi’ar akasarin masu wadata na ci-kai-kadai, rayuwar almajirci, lalacewar harkar ilimi, shaye-shaye na matasa, siyasa, handama, cin hanci da rashawa da dai tarin abubuwa da dama wanda kamar yadda na ambata tun farko kusan a na iya cewa babu wani shafi na rayuwar mu ta yau da shirin Dadin Kowa bai taba ba.

 

Sai dai dukda kowane sashe na shirin yana da alaka da rayuwar al’ummar mu kai tsaye abu mafi girman daukar hankali wanda kuma kan shi ne na fi jinjinawa marubutan shirin shi ne yadda suka tafiyar da shi bisa tsari na haskowa al’umma manya-manyan kalubalen da a rayuwar mu ta zahiri su ne suka addabe mu a yau kusan ma fiye da komai. Wanda a dunkule idan a na so a ambaci wadannan manyan kalubalen shi ne ake kiran su da suna ‘matsalar tsaro’. Hakika marubutan shirin sun yi kokari kwarai matuka wajen wayar da kan al’ummar dake gari da ma na kauyuka kan shi wannan fanni na matsalolin tsaro da kuma yaduwar ayyukan ta’addanci wanda su ne manyan barazanar da kasashen mu suke kan fuskanta a yanzu.

 

Idan muka dubi matsalar Boko Haram wanda shi ne babbar matsalar tsaro na farko da shirin ya fara bayyanawa kasantuwar ita ce matsalar tsaro ta farko da ta fara kunno kai a shiyyar arewacin Najeriya da kawo yanzu aka kwashe shekaru a na fama da ita, za mu ga cewa duk da kasancewar daukacin marubutan shirin mazauna Kano ne ba wai ‘yan asalin jihohin da matsalar ta fi tasiri ba ne, hakan bai hana su yin bincike ba akan lamarin wanda a yadda suka tsara rubutun kai kace wani mazaunin Yobe ko Borno ne ya rubuta musu duk wadannan gurare masu alaka da ta’addancin kungiyar saboda matukar kokarin da suka yi kama daga kan yanayin yadda suka shirya faruwar al’amura mabambata tsakanin jaruman shirin wadanda suka fito a matsayin ‘yan ta’adda da kuma jama’ar gari har ma ga kai wa ga samuwar ‘yan gudun hijirar da aka bayyana cewa sun baro muhallansu ne a sakamakon ta’azzarar rikicin wanda dukkan su abubuwa ne da da za a ce hoto ne na abinda suka faru da mazauna shiyyar arewa maso gabshin Najeriya a zahiri domin wasu har kwanan gobe a matsayin ‘yan gudun hijirar suke ba su kai ga komawa muhallan su ba.

 


Ni kai na da nake wannan rubutun tsohon dan gudun hijirar ne a sakamakon ita waccan matsala kuma kodayake a yanzu lamarin abu ne da ya zama tarihi, kallon hakan da na yi a cikin shirin ya tuna min da faruwar al’amura da dama na wahalhalun dake da akwai ga wanda dare daya dole ta tilasta masa yin gudun ceton rai tare da barin muhallinsa ba tare da shiryawa hakan ba duk kuwa da cewa akwai tarin abubuwan da ya kamata shirin ya nuno a game da lamarin wanda ba a samu hakan ba.

 

Karin wani babban al’amarin har wayau kan dai shi wannan lamari na matsalar tsaro da kuma ballewar ‘yan ta’adda a cikin shirin shi ne na batun masu garkuwa da mutane wanda shi ma matsala ce da a yanzu ta addabi wasu jihohin na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya da yawancinsu ke makotakata da kasar Nijar. Inda kuma lamarin ke tafiya daidai da yadda suka wayar da kan al’umma a baya bisa abubuwan da suka shafi ‘yan Boko Haram haka a yanzun ma suke kan wayar wa masu kallo kai kan lamarin na masu garkuwa da mutane tare da nuna irin fadi tashin da dangin wanda aka kama suke shiga da kuma irin wahalhalun da su wadanda aka yi garkuwa da su din suke shiga.

 

Sai dai inda gizo ke sakar a nan shi ne kusan a na iya cewa akalar shirin ya fi karkata ga bayyana matsalolin da suka yi wa al’umma katutu ba tare da kyakkayawan tanadi na ganin karshen su ba. Ma’ana zubin rubutun ya fi kafuwa da kuma ginuwa akan nishadi da kuma hasko matsalolin ne kawai sama da nuna matakan warware su misali har aka lafar da batun matsalar tsaro na farko a cikin shirin babu wata hanya takamammiya da a ka bi wajen shafe tarihin Boko Haram ko kuma wani yunkuri da shirin ya nuna da watakila zai zama zaburarwa ne ga jama’ar kasa ko gwamnati ko kuma su jagayyar yaki da ta’addancin wato jami’an tsaro ko ma dai dukka bangori ukun da za a ce shirin zai sa a tasirantu da wannan abu da ya kawo din har ma ayi yunkurin jarrabawa a zahirin don ganin ko za a dace a kawo karshen matsalar ko kuma rage mata karfi.

 

Hakanan  ma ta bangaren matsalar masu garkuwa da mutane muna tunanin a wannan karon za a samu sauyi sai ga shi a karshe dai tarihi ne ya maimaita kansa wato babu wani hobbasa da shirin ya bayyana na radin kansa na ganin cewa karshen matsalar ta zo ta hanya mafi samar da nutsuwa yadda al’ummar dake kallo za su ji da zaran an bi irin wannan hanyar to za a shafe babin ‘yan ta’addan dake garkuwa da mu daga doron duniya kuma ba za a sa ran wasu zasu sake sake sha’awar kwatanta irin hakan ba har na tsawon wasu zamanunnuka masu zuwa a gaba.


 

Abin marubutan shirin Dadin Kowa ya kamata su fahimta su kuma sani shi ne, karfin tasirin da suke da shi bisa zukatan al’umma na juya  akalar tunanin su ya fi wanda ‘yan sanda da gwamnati take da shi. Ya ishe mu misali abin dogaro yadda a wajen gabatar da al’amuran mu na yau da kullum muke cin karo da ire-iren mutanen da suke karyata gwamnati ko jami’an tsaro kan sha’anin tsaron kasa da sauran al’amuran rayuwa wanda har hakan ke sa daukacin ‘yan kasar da dama mika wuya gami da sallamawa cewa a haka rayuwa za ta cigaba da murzawa ba tare da an ga karshen wadannan manyan matsaloli na tsaron ba har zuwa lokacin da duniya za ta tashi saboda komai ya fito daga bakin jami’an gwamnati ko jami’an tsaro daukar batun ake a ta zo mu ji ta. Amma cikin sauki ire-iren wadannan mutane za ka ga suna yanko har misalai da wadansu abubuwan da suka faru a shirin inda hakan ke nuna mana cewa a saukake zukatan su ke tasirantuwa da shirin har ma suke rikar shi a matsayin abin kafa hujja.

 

Ga wasu muhimman abubuwa da nake so mu fara kalla tukunna dangane da tasirin shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24 kafin na kai ga bayyana ainihin makasudin abinda ya sanya ni yin wannan rubutun:

·        Kowa yayi imanin cewa a yanzu haka shirin Dadin Kowa ya samu karbuwa fiye da duk wasu shirye-shirye ko fina-finai da ake kan yi a masana’antar Kannywood; karbuwa irin wanda manya da yara, tsofi da matasa, ‘yan boko da kolawa, mazauna birni da kauyuka duk suka yi tarayya a wajen son kallon shirin tare da bibiyarsa.

 

·        Mutane sun tasirantu da shirin saboda kamanceciyar da yake da rayuwar su ta zahiri duba da cewa ya ginu ne akan haska irin rayuwar da suke ciki ne kai tsaye ba wai ya ginu ba ne ga kage-kage ko kirkirar irin abubuwan nan wanda daga kallo ma mutum zai ce wannan ai sai dai a wasan kwaikwayon. Inda hakan yasa a saukake zukatansu ke amanna da kuma yin na’am da duk abinda suka gani cewa lalle a gasken ma haka ne ke faruwa.

 

·        A duk lokacin da wata matsala ta bijiro dokin ‘yan kallon karuwa yake tare da zuba idon ganin ta hanyar da za a warware matsalar wanda hakan ke nuna cewa akwai wani nau’i na sa rai ko yakini da mutane ke da shi akan shirin na cewa mafitar da suka ga an bi wajen warware wani al’amari a cikin shirin na iya zama irin hanyar da za su bi kenan wajen warware matsalolin tasu rayuwar wannan yasa daukacin masu shirin ba sa yarda daidai da na kwana daya shirin ya wuce su. Idan muka duba misalan irin yadda abubuwa suka faru kama daga rikita-rikitar Alhaji Mala da wajen aikinsa, batun Nasir da Stephanie, Headmaster da E.S, Bintu da Ibrahim, Malam Musa da matansa wannan duk misalan wasu kananan abubuwa ne da faruwar su a cikin shirin ya sauya yanayin zamantakewar mutane da dama tare da sauya musu ra’ayi.

To ashe kuwa duba da wannan bayani kai tsaye a na iya cewa shirin Dadin Kowa ga al’ummar wannan zamani tamkar wani jami’in tsaron ne mai zaman kansa dake aikin jagorantar al’umma wajen nusar da su halin da suke ciki da kuma fahimtar da su girman matsalar dake damun su abinda kawai shirin ya rasa shi ne kasa jagorantar al’umma masu kallon nasa da dabarun da za su fita da daga wannan matsala da suke ciki wannan kuma shi ne abinda nake nufi da rauni ko gazawar shirin a cikin shi wannan rubutun.

 

Kasancewar batu ne da yake da yawa da kuma fadin gaske zan so a ku dakonce ni zuwa gobe insha Allah inda zan kawo mana hakikanin raunin shirin da kuma abinda ya fi kyautuwa a ce shi ne abinda marubutan shirin suka bayyana wa ‘yan kallo a matsayin hanyoyin dakile matsalar tsaron da aka nuna a ciki a maimakon wannan abu mai kama da almarar da aka yi mana cikin shirin wanda aka haska jiya da cewa an kai ga kama ‘yan ta’adda da shi.

Reactions
Close Menu