“Buri na rubutuna ya zama rayayye ko bayan ni ba na raye” – Haruna Birniwa

 

Haruna Rabiu Suleiman

 

H

ARUNA RABIU SULEIMAN wanda aka fi sani da Haruna Birniwa daya ne daga cikin matasan marubuta littafan Hausa masu tasowa dake jihar Jigawa inda kawo yanzu ya kai ga samun nasarar wallafa wasu rubuce-rubucen nasa zuwa littafi. A wannan hirar ta su da wakilin Mujallar ADABI, Musaddam Idriss Musa za a ji tarihin matashin da kuma yadda aka yi ya fara rubutu. Ga yadda hirar ta su ta kasance:

 

Makarantanmu za su so su ji tarihin rayuwarka

 

Suna na Haruna Rabiu Suleiman, ni haifaffen garin Birniwa Tasha ne, wani dan kauye a gefen garin Birniwa. Na yi karatun boko da islamiyya a garin har izuwa matakin sakandire, daga nan na koma kano dimin share fagen shiga jami'a a makarantar CAS ta Kano. A takaice dai yanzu ina karanta ilimin kimiyyar kyamistari (Chemistry) a reshen Jami'ar Bayero dake garin Gumel a Jihar Jigawa.

 

Tun yaushe ka fara harkar rubutu kuma ya aka yi ka tsinci kanka a lamarin?

 

Na fara rubutu tun ina dan aji 6 na firamare, zan iya tuna littafin Ibada da Hukunci na samu nake kwafewa sai na ce na rubuta littafi, kuma har nai ta murna. Hahaha! Na fara rubutun littafi ka'in da na'in a 2008.

 

Zuwa yanzu ka rubuta littattafai nawa?

 

Na rubuta littattafai rututu, domin kuwa al'adata ce na rubuta littafi cikin hard cover na baiwa aboki ko kawa tun da a lokacin ban san  buga shi ba, saboda yarinta ta. Bayan zamana a Kano 2014 sai na fahimci zan iya rike rubutu a matsayin sana'a daga nan sai na fara rubutawa ina ajiyewa. A yanzu na rubuta littattafai tara, shida na soyayya ne, biyu na zamantakewa, dayan kuma na rubuta ne wa Sarkin Kano, Mai martaba Sir Sanusi na biyu.

 

Wane littatafin ka zaɓa a matsayin bakandamiyarka?

 

‘Burgami A Hannun Beraye’ domin na fuskanci kalubale akansa.

 

Mene ne babban burinka a rayuwa?

 

Buri na rubutuna ya zama rayayye bayan ni ba na a raye.

 

Me ya fi burge ka a rayuwa?

 

Musu a tsakanin masana a harkar ilimi.

 

Wane sako kake da shi zuwa ga makaranta da masoyanka?

 

Sakona ga makaranta na shine su ci gaba da karatu da nazarce-nazarcen ilimomi, domin duniya da mutum biyu take alfahari; mai ilimi da mai nemansa.

 

 

 

Reactions
Close Menu