Jaruma Hafsat Idris ta mallaki dalleliyar mota 'yar yayi

 

Jaruma Hafsat Idris cikin sabuwar motarta (Hoto daga shafin Instagram na officialhafsatidris)

Fitacciyar jarumar fim ɗin nan a masana'antar Kannywood, Hafsat Idris ta ɓaro dalleliyar mota ta zamani ƙirar 4matic kamar yadda ta ɗora hoton motar a shafinta na 'Instagram' a jiya Alhamis.


Jarumar wadda ta yi fice da fim ɗinta mai suna 'Ɓarauniya' ta daɗe da shiga jerin manyan matan Kannywood da dake tashe sai dai a yanzu a na iya cewa ta faɗa a sahun jerin na gaba-gaba dake wanka da Naira.


 Tuni dai sauran abokan sana'arta suka shiga yi mata addu'o'in sanya alkairi gami da nuna farin cikin wannan gagarumin cigaban da jaruma Hafsat Idris ɗin ta samu a cikin wannan wata na azumin da muke ciki. Inda daga cikin masu tayata murnar akwai manyan daraktoci na masana'antar da furodusoshi haɗi da ƴan uwanta jarumai maza da mata.

Reactions
Close Menu