‘Na zabi rera wakar Hip-Hop ne saboda burin ganin na fitar da sabon abu’ – Adam MGZ

Adam Muhammad MGZ


A

dam Muhammad MGZ matashin mawakin Hiphop ne da ke rera wakokinsa da harshen Karaikarai wanda kuma a yanzu ya shahara a wannan fanni. Ana iya cewa mawakin ya zo wa al’ummar wannan harshen da wani sabon salo kasancewar daukacin mawakan dake amfani da harshen wajen rera wakokinsu yawanci wakokin nasu na tafiya ne bisa salon wakar RnB ko kuma nanaye kamar yadda ake kiran salon da harshen Hausa. A cikin wannan tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilin mu MUSADDAM IDRISS MUSA da kuma mawakin, za ku ji bayanin tarihinsa, yadda ya zama mawaki da kuma dalilin da yasa ya zabi salon wakar Hiphop a wakokinsa da yake ta shi wannan harshe na Karaikarai;

 

 

Da farko zamu so mu san cikakken sunanka da kuma tarihin rayuwarka a takaice?

 

          Suna na Adamu Muhammad wanda ake wa lakabi da "MGZ". Ni dan garin potiskum ne kuma mazaunin unguwar central hotel a jihar Yoben Najeriya. Na yi makarantar firamare dina a karamar hukumar Nangere kafin daga bisa ni na dawo garin Potiskum inda na yi karamar sakandire dina a wata makaranta mai zaman kanta (private school) da ake kira Imam Malik Junior and Senior Secondary School. Bayan na gama shekaru uku na a can sai na sake komawa Sabon Garin Nangere a can karamar hukumar Nangere din wato garin da na yi firamare inda na dora da karatun babbar sakandire dina a makarantar Government Secondry School (GSS) Nangere. A halin yanzu shekaruna ashirin da biyu 22 a duniya matakin karatuna kuma sakandire amma na rubuta jam bana inda zan cigaba da karatu na a matakin difiloma.

 

Tun yaushe ka fara sana'ar waka kuma me ya ja hankalinka wajen zama mawaki?

 

          Na fara harkar waka ne tun a shekara ta dubu biyu da sha hudu (2014). Abin da ya ja hankalina na fara harkar waka kuwa wannan kuma nufi ne na Allah saboda a lokaci guda na ji ina son na fara din, don ba zan manta da wata rana ba ina zaune na ina sauraron wata wakar aure da aka yi wa wani yayana sai kawai na ji a raina cewa zan iya wakar auren nima ta yaren Karai-karai, daga nan sai kawai na rubuta na je wajen da ake aikin buga wakokin aka min aikin wakar.

 

Wannan wakar auren da ka yi da yaren Karaikarai ana iya cewa da ita ka fara?

 

          Kwarai kuwa, haka ne.

 

Kawo yanzu da ka shafe wasu shekaru kana waka,  shin wakokinka za su iya kai nawa?

 

          Na yi wakoki da dama kuma a kalla yawansu zai kai dari da hamsin (150). Daga ciki akwai wadanda na yi su ne da harshen Hausa don kusan sune ma suka fi yawa don wadanda na yi da yaren Karaikarai din ba su fi guda goma sha biyar (15).

 

A baki daya wakokin naka da ka yi, wadanne daga cikinsu ne za a kira a matsayin fitattun wakokin ka da suka fi shahara?

 

          Fitattu daga wakokin da na yi akalla sun kai biyar. Daga ciki akwai: Kuwāi (bai mālā), Rabjano, Nafatenenako, Aine da kuma Bazino. Su wadannan dukka wakoki ne da na yi su da harshen Karaikarai.

 

Duba da cewa wakokin naka anyi su ne da harshen Karaikarai, shin za mu iya sanin sakonnin da suke isar wa ga al'umma?

 

          Abinda ita kalmar 'bai mālā' take nufi a harshen Karaikarai shi ne Duniya wato sakon wakar an gina shi ne akan rayuwar duniya. Wakar Ràbjano kuma tana nufin budurwata, ita kuma Bāzìno tana nufin samari wato matasa.

 

Me ya ja hankalinka na zabar salon wakar Hip-hop wajen rera wakokin naka na yare?

 

          Ni wakokin Hip-Hop nake yi amma da harshen Karaikarai. Abinda ya ja hankalina na fara wakokin Hip-Hop da harshen Karai-karai maimakon Hausa shi ne a lokacin da muke tare da wasu gayuna (abokai) wanda su dama tuntuni wakokin Hip-hop suke yi ni kadai ne mai yin wakokin nanaye wanda kuma su ma yawanci a lokacin ta harshen Karaikarai din nake yin su daga baya ne kuma sai na ji ra'ayina ya canja, ya zama na koma ina son rera wakokin Hip-hop ta yare sakamakon burina na son ganin na fitar da wani sabon abu saboda masu yin Hip-Hop da harshen Hausa sun fi yawa.

 

Ko ta taba fuskantar kalubale a harkar waka da kake yi?

 

          Kwarai. Kafin na fara harkar wakoki na ga kalubale da dama haka ma kuma a lokacin dana fara. Ban yi tunanin zan kawo yanzu ba a harkar saboda rashin masu ba ni karfin gwiwa, amma a yanzu alhadulillah, wadanda suke karfafa min gwiwa su ne su ka fi yawa.

 

Wane buri kake da shi game da harkar wakokin Hiphop da kake yi na yare?

 

          Babban burina shi ne duniya ta san su waye Karaikarai sannan na zamo abin alfahari wajen ‘yan uwana masu yaren, ina kuma da burin ganin na zama sanadi na samuwar farin cikinsu ta ko yaya.

 

 

Reactions
Close Menu