“Sai inda ƙarfina ya ƙare a fagen taimakawa ƙananun marubuta” - Hafsat Azare

Marubuciya Hafsat Umar Azare

 

S

hahararriyar marubuciyar harshen Hausan nan kuma gogaggiyar ƴar jarida kana kuma shugabar zauren Hausawan Afirka na reshen jihar Bauchi, Hajiya Hafsat Umar Ɗan Tanko Azare ta lashi takobin cigaba da tallafawa gami da taimakon ɗaukacin ƙananun marubuta masu tasowa dake zaune a faɗin jihar Bauchi da ma kewaye.

 

Marubuciyar wadda ta samu shaida sosai daga ɗaruruwan mutane a cikin faɗin jihar ta Bauchi dama sauran jihohin arewa, kai harda ma mutane mazauna wasu ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya a kan halayyarta na kishin harshen Hausa da kuma dagewa wajen bayar da gudummawa da dukkanin damar da take da ita, ta ƙara tabbatatar da aniyarta na cigaba da ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ta taimakawa marubuta masu tasowa don tsayawa a bisa dugadigansu.

 

Jawabin na ta dai ya gudana ne a yayinda a ka gudanar da taron kafa ƙungiyar marubutan Hausa na jihar Bauchi inda marubuciyar ta zamo shugabar ƙungiyar ta farko.

Reactions
Close Menu