‘Tauye 'yanci ne yasa hukuma take kama marubuta a Saudiyya’ - Yahya Assiri

Yahya Assiri
 

W

ata kungiyar kare hakkin Dan Adam na 'yan kasar Saudiyya mazauna birnin Landan ta soki hukumar kasar Saudiyya biyo bayan kame wasu marubuta guda takwas da 'yan sandan kasar na fararen kaya suka yi a kwanan bayan nan.

 

Da yake bada tabbaci kan kama marubutan da hukumar kasar ta Saudiyya din ta yi, shugaban kungiyar Yahya Assiri, ya bayyana cewa, marubutan wanda adadin su ya kai 8 sun hada da Bader Al-Rashed, Sulaiman Al-Saikhan Al-Nasser, Waad Al-Mohaya, Musab Fouad Al-Abdulkarim, Abdul Majid al-Balawi,  Abdulaziz Alehis, Abdulrahman Monthly da kuma Fouad Al-Farhan. Dukkanin su mazauna biranen Riyadh ne da kuma Jeddah, kowannen su kuma har gida aka je aka kama shi ba tare da bayyana takamaimen dalili na yin hakan ba.

 

A cikin sakon da ya aikawa Aljazeera ta hanyar kibdau Assiri ya ce, "mutane za su yi ta tambayar dalilin da yasa ake kama mutane a yanzu. Amma gaskiyar ita ce hakan na nuni ne da yadda al'umma a kasar suke zaman kunci da gallazawa tsawon shekaru,"

 

"Kamar dai kamen da aka yiwa manyan maluman addinin musulunci a watan Satumban 2017, da wanda aka yiwa masu fafutukar kare 'yancin mata a shekarar 2018, da kuma wanda aka yiwa 'yan fafutuka a kasar cikin watan Afirilun 2019. Wadannan marubutan da aka kama a kwanakin baya-bayan nan su ne na karshe a rukunin mutanen da aka dana tarko don a garkame su" inji Assiri

Hukumar Riyadh ta musanta zargin cewa ta kama fursoni bisa bayyana akidarsu ta siyasa da ta sha bamban da tata, amma kuma manyan jami'an hukumar jihar sun bayyana cewa don tabbatar da wanzuwar zaman lafiyar kasa, garkame masu nuna kin jinin mulkin kasar da sa ido akan sauran 'yan fafutukar dake sukar gwamnati abu ne da ake bukatar shi.

 

Wadanda aka tsare din dai ba sa daga rukunin 'yan sahun gaba na masu nuna kin jinin mulkin kasar. Yawancin su marubuta ne na mukalu da ake wallafawa a jaridu sai kuma wadanda ake hira da su a gidajen talabijin.

 

Irin wannan yanayin da ake ciki a Saudiyya din dai ya karkato da hankulan mutanen duniya inda gwamnatin kasar karkashin jagorancin Yarima Mohammed bin Salman ke cigaba da shan suka musamma duba da yadda a yanzu kasar ce take shugabantar kungiyar kasashen yankin guda 20.

 

Manazarta daga kasashen duniya suna zargin gwamnatin kasar Saudiyyan da kokarin musgunawa masu adawata da ita a siyasance inda har wasu ke ganin cewa matakin da hukumar kasar ta dauka a baya-bayan nan kan yaki da rashawa ba komai ba ne illa yunkurin kawar da manyan 'yan kasuwa masu karfin arziki wanda adawar su ke neman kawo tangarda ga mulkin kasar.

 

A halin yanzu dai Saudiyya na cigaba da fuskantar suka daga kasashen duniya bayan shigarta jerin kasashe masu dakile 'yancin fadar albarkacin baki da kuma tauye 'yancin 'yan kasa da suka hada da kisan dan jaridan da jami'an kasar suka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi shekarar da ta gabata da kuma barin wutar da tayi kan kasar Yemen.

Reactions
Close Menu