"Tun Ina Ƙarama Na Taso Da Sha’awar Harkar Fim" – Rahama M K

Rahama MK (Hoto daga shafin Instagram na realrahamamk)


Ba tun yau ne ba akalar finafinan Hausa ta sauya alkibilar ta inda a yanzu finafinai masu dogon zango da ake haskawa a tashoshin talabijin suka zamo kan gaba wajen jan ragamar harkokin bakiɗaya. Wannan dalili ne yasa jaruman da suke kan tashe da kuma haskawa a duniyar fim na yanzu suka kasance ire-iren jaruman dake taka rawa a nau'ikan waɗannan shirye-shirye ne. Jaruma Rahama MK dake taka rawa a shirin Kwana 90 na tashar Arewa24 a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ɗaya ce daga fitattun jarumai mata na masana'antar dake kan tashe a yanzu.

Domin jin tarihin rayuwar ta da kuma yadda ta samu kan ta a cikin harkar fim, wakilin mu ya tattaro mana wannan rahoto kan tattaunawar da jaridar Leadership tayi da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.


Rahama M K. To da farko dai suna na Rahama Mukhtar Sulaiman wadda aka fi sani da Rahama M K, Kuma an haife ni a shekarar 1987 na yi makarantar firamare a ABU Zaria Staff School. Na fara Sakandare a GSS Shika na karasa a Eleganzer International School da ke Kano. Na yi Diploma a Annur Islamic Institute ABU Zaria, kuma na yi aure ina da yara biyu a Jos. Ina kuma aiki a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano.Ya ya aka yi kika samu shiga harkar fim?


Yadda na samu shiga harkar fim dai shi ne akwai wata ‘yar uwa ta wacce ta ke harkar fim Aisha Tafida Gombe wadda ganin ta ne a cikin fim ya sa na fara sha’awar shiga harkar, kuma na fara harkar fim din Hausa a 2013 in da na fara da fim din Aminai, sai Nisan kiwo da kuma wani fim Ka ci amanata. Amma dai tun ina karama ina da sha’awar harkar sai dai ita Aisha ta karfafa mini gwiwa ne, don haka na taso ina sha’awar harkar fim kuma na gamsu da za ka iya isar da sako ka kuma ilmintar sosai. A bangaren wannan shi ne abin da ya sa na shiga kuma na yarda cewar sana’a ce shi ya sa na fara.


Rahama MK (Hoto daga shafin Instagram na realrahamamk)
To ya aka yi kika samu shiga shirin Kwana Casa’in ?


E akwai Abdulkarim Papalaje, shi ne wanda na ke gani a matsayin Uban gidana tun da Usman Mu’azu ya hada ni da shi a matsayin Manaja na shi ya sanar mini za a fara tantance masu son shiga aikin kwana Casa’in din, don haka ta hanyar sa ne na samu shiga cikin shirin Kwana Casa’in kuma na yi sa’a na samu wannan rol na Matar Gwamna wadda a yanzu duk duniya aka sanni da shi.To ya kika ji a matsayin ki na jaruma da kika hau rol din Matar Gwamna?


Gaskiya na ji dadi sosai na kuma godewa Allah da ya sa na samu wannan rol din kuma ina alfahari da shi.domin yadda mutane su ke girmama ni da kuma yadda su ke kallo na a matsayin babbar mace mai aji shi ya fi burge ni don haka ina jin dadi sosai.Da ya ke yanzu kin zama babbar Jaruma za a iya cewa burin ki ya cika?


Rahama MK (Hoto daga shafin Instagram na realrahamamk)Alhamdulillah buri na ya cika sai dai godiya ga Allah, a Koda yaushe ina Kara gode masa Alhamdulillah. Domin kuwa a dalilin fim din na yi gida, na yi mota, aikin Hajji na ke da burin na je a yanzu in sha Allahu. Don a yanzu ko’ina na je wucewa mutane na farin ciki da zuwa na saboda da sun gan ni, ko’ina na wuce daga me cewa Matar Gwamna sai masu cewa Fulanin Bawa Mai kada, ina alfahari da Ni’imar da Allah ya yi mini Alhamdulillah.Menene sakon ki na karshe ga jama’a?


To sako na dai bai wuce na yi wa masoya na godiya ba saboda irin kaunar da su ke nuna mini domin duk wani abu da na zama a rayuwa ta sanadin kaunar da su ke yi mini ne, don haka nagode sosai Allah ya bar mu tare da su.

Reactions
Close Menu