Jarumar Kannywood ta bada labarin soyayyarsu da tsohon shugaban ƙasar Najeriya

 


Shahararriyar 'yar wasan Hausan nan da a makonnin baya ta shaidawa duniya cewa tana jin kamar ta kashe kanta saboda damfararta da aka yi na miliyoyin kudi, jaruma Ummi Ibrahim da aka fi sani da laƙabin Zeezee ta kuma fitowa ɓaroɓaro tare da shaidawa manema labarai cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janaral Ibrahim Badamasi Babangida IBB tsohon saurayinta ne.Rahoton wanda jaridar yanar gizo ta Neptune prime ta ruwaito daga mujallar Daily Trust's Weekend Magazine ya nuna kalaman jarumar na cewa

tsohon shugaban ƙasar Najeriya a lokacin mulkin soja, Janaral Ibrahim Badamasi Babangida IBB  saurayina ne a da amma banda yanzu. Sai dai muna mutunta juna har zuwa yanzu a matsayin abokanai.


Jaruma Ummi Zeezee ɗin ta ci gaba da bayyanawa manema labaran cewa

A yanzu ina da saurayi da ba a masana'antar nishaɗi yake ba da a yanzu muke shirin auren juna idan Allah ya so.

Reactions
Close Menu