JISWA ta ƙaddamar da littafin 'Tarihin Garin Majiya'

Daga wakilin Mujallar Adabi a jahar Jigawa

Bodmas Abu Hammad Hadejia

A Ranar 15/05/2021 aka kaddamar da littafin tarihin garin Majiya dake yankin karamar hukumar Taura, wanda Malam Sani Gambo Majiya ya rubuta.

Da take gabatar da taliki akan littafin Dakta Binta Umar ta kwalejin ilimi ta jiha dake Gumel, tayi dogon bayani akan dangantakar Majiya da sauran garuruwa a jihar Jigawa.

Tace al`ummar Majiya suna da dangantaka da garuruwan, Gumle da Kazaure da Kiri da kuma Gunka.

Sanata Dan-Ladi Sankara yafi kowa sayan kwafin littafin da aka kaddamar inda ya sayi kwafi ashirin na littafin akan kudi naira dubu dari biyu, sai Alhaji Ado Sani Kiri ya sayi kofi biyar akan naira dubu dari da hamsin.

Sauran wadanda suka sai littafin akwai, Alhaji Musa Adamu Majiya mai jami`ar Khadijah da Alhaji Habibu Abdurrahman Majiya da Honourable Dan-Gabi Kwalam da Alhaji Haruna Mai Fata Kwalam dukkanin su sun sai kwafin littafin akan kudi naira dubu dari-dari kowannan su, yayin da Alhaji Gambo Gujungu ya sayi kwafi goma akan naira dubu casa`in da tara.

Mai martaba sarkin Ringim, Alhaji Sayyadi Abubakar Mahmud ya sami wakilcin Chiroman Ringim, Alhaji Usman Abubakar, yayin da Sanata Danladi Sankara da Ado Sani Kiri suka aike da wakilansu a lokacin kaddamar da littafin.

Reactions
Close Menu