"Ba don Abdul Amart ba da mun zama mabarata" in ji 'yan Kannywood

Abdul Amart Maikwashewa

Jarumai da mawaƙan masana'antar fina-finan Hausa da ake wa laƙabi da suna Kannywood sun nuna amanna gami da yarda da furucin da ɗaya daga manyan Daraktocin masana'antar Sanusi Oscar442 inda ya bayyana cewa dukkan 'yan masana'antar a halin yanzu tuni da sun zama mabarata in ba don albarkacin furodusa Abdul Amart Maikwashewa ba.


Oscar 442 ya bayyana hakan ne a shafinsa na kafar sada zumunta inda ya rubuta sakon nasa kamar haka:

Ba don Abdulamart ba da yanzu 'yan Kannywood mabarata ne.

 

Darakta Sunusi Oscar 442


Darakta Oscar ɗin ya kuma rubuta ƙarin bayani a ƙasan shi wannan rubutun nasa da cewa

Wannan ra'ayi na ne, ku biyo ni a sannu za ku ji dalilin da yasa na faɗi haka.

Tuni wasu fitattun jarumai a masana'antar da suka haɗa da Hamza Talle Maifata, Halima Atete, Mustapha Naburaska, Garzali Miko dasauran jarumai suka nuna gamsuwa da kuma amincewa da kalaman daraktan. Sai dai akwai alamun akwai wasu sashe na jaruman dake jiran fara ganin dalilan daraktan na faɗar hakan tukunna kafin su bayyana gamsuwar su ko akasin haka.

Abdul Amart dai ɗaya ne daga manyan masu shirin fim a masana'antar kuma shi ne shugaban kamfanin Amart Entertainment sannan yayi ƙaurin suna wajen shiri na waƙoƙin siyasa.


Shin mene ne ra'ayinku kan wannan batu? Kuna iya bayyana mana ta inda aka rubuta comment a kasan wannan post ɗin.Reactions
Close Menu