"Ban ga aibu ba tattare da auren marubuci" in ji Fatima Aminu Ya'u

 


Fatima Aminu wadda aka aka fi sani da lakabin ‘Faɗima Fayau’ matashiya ce kuma fitacciyar marubuciya a yanar-gizo da ta tara dubbannin masoya, makaranta littattafanta. A wannan tattaunarwar da tayi da wakilin Mujallar ADABI, Musaddam Idriss Musa yayi da marubuciyar wadda ta kasance daliba a Jami’ar Bayero dake Kano ta bayyana mana yadda tafiyar ta a duniyar rubutu ta faro, kalubalen da ta fuskanta, burinta a yanzu da ma karin wasu abubuwa da dama. Ga yadda hirar tasu ta kasance;

 

Mujallar ADABI: Da farko masu karatu zasu so jin cikakken sunan ki tare kuma da tarihin rayuwarki har izuwa inda kika fara amsa shi wannan suna na zinare wato 'marubuciya'.

Fatima: Assalamu alaikum, Suna na Fatima Aminu Ya'u. Haifaffiyar garin kano ce kuma na yi dukkan karatuna bakiɗaya a nan garin Kano. Inda yanzu haka nake Tsangayar Koyon Noma dake nan Jami’ar Bayero University ta garin kano. Eh to da fari na fara rubutu ne saboda gasa….eh zan kira shi gasa, don lokacin da muna karamar sakandire ajin mu ya karkasu ne; wasu kan yi irin littafin girke-girke, wasu kuma na wake-wake, to mu sai muka zaɓi mu rubuta labari duk wadda ta yi za ta ba wa kawayenta su karanta, in bai yi dadi ba ko in yayi shirme da yawa za'a mata dariya, wannan ina maka maganar Jss 2 ne. Bayan mun zo Jss 3 sai na Fara wani littafi nasa masa Saddikha wato sunan jarumar, amma na Hausa ba kamar na baya da muke na Turanci ba, kotsam ran nan Babanmu ya gani 

Cikakken rubutu da ya amsa sunansa rubutu na fara shi ne a JSS 3 wanda zuwa yanzu da ake magana, na rubuta littattafai 14 biyu daga ciki ina kan yin su ne a yanzu, na rubuta littafai huɗu na Turanci sauran kuma dukka na Hausa.

Sai ya karɓa ya duba, bayan ya gama karantawa yace na ba shi zai bayar don a duba, shi ne ya kai wa wani ya gyara, yayi editing da typing, da komai dai. Ya canja masa suna zuwa Yanayin Rayuwa. A takaice na fara rubutu tun Jss 2 amma cikakken rubutu da ya amsa sunansa rubutu na fara shi ne a JSS 3 wanda zuwa yanzu da ake magana, na rubuta littattafai 14 biyu daga ciki ina kan yin su ne a yanzu. Na rubuta littafai huɗu na Turanci sauran kuma dukka na Hausa da suka hada da: Yanayin Rayuwa, Haka Nake Sonki, I Don’t Care, Amratu da dai sauransu.

Mujallar ADABI: Masha Allah, ashe ina tare ne da malamar gona don haka ba buƙatar na ji faduwar gaba a damunar bana. Shin ya batun iyali fa ban ji kin haɗo da wannan fannin ba ko dai don a masu karatun mu akwai mata ne kina kishin ka da su karanta miki sunan miji?

Fatima: (Dariya) Har ka ban dariya. Yo meye a ciki don an karanta sunan sa, da akwai shi da ba abinda zai hana ni sa sunan nasa. Aure tukunna, fatan makaranta zasu taya mu addu'ar samun na gari.

Mujallar ADABI: tawa har ta riga ta makarantan na mu ma, Allah ya kawo nagari, mu kuma zamu zo taron bikin ko ba katin gayyata tunda amarya aka ce ba ta laifi.

Fatima: To, ina godiya da addu'a.

Mujallar ADABI: duba da yadda kika taso da kuma dalilin da ya kai ki ga zama marubuciya. Shin ko a yanzu kina ji a ranki cewa dalilin da ya sanya kike yin rubutu a yanzu ya sauya da yadda kike ji a da can baya?

Fatima: Eh to a da na fara don ina so ne kawai, sai dai a yanzu dalilin karuwa yayi kawai amma na bayan yana nan wato bai canja ba. Ina son rubutu ina kuma da abubuwa da yawa dake wakana a zuciya ta wanda ta hanyar rubutun ne kawai zan iya fitar da shi ga mutane don su karanta kuma su karu da yar guntuwar fahimta ta game da rayuwa.

Mujallar ADABI: Akan samu marubuta littattafai da a lokaci guda kuma su kan kasance marubutan wakoki, shin ko ke ma kina daya daga cikin su?

Fatima: A’a, ba na waka hasali ma ni ba ni da wata sha'awa akan waka.

Mujallar ADABI: Wadansu na ganin cewa akwai aibu marubuciya da marubuci su yi aure inda suke shan alwashi na gujewa faruwar hakan. Shin naki ra'ayin ya zo ɗaya da nasu ko kuwa dai kun bambanta?

Fatima: Dukda dai ban san dalilin masu ganin aibun hakan ba, ni a guri na babu aibu gaskiya, domin ni mutun ce mai son tattauna abinda nake son rubutawa da wanda muke tare. Marubuci ne zai fahinci me nake magana akai yake kuma da lokacin taya ni tunanin abin da nake rubutawa din. 

Mutumin da yake rubuta yadda gida ke zama cikin walwala idan miji na bada kulawa ina ganin a zahiri zai fi kowa iya aiwatar da abinda ya rubuta, ita kuma burin mace daman samun mijin da ya san darajarta ne wannan kuma ina ganin marubuci na gaba-gaba wurin sanin darajar ‘ya mace.

Ni a matsayi na na me taɓa rubutu kullum ina son na ga na aiwatar da wasu abubuwan da nake rubutu akai sai nake ganin marubuci namiji ma hakan ne. Mutumin da yake rubuta yadda gida ke zama cikin walwala idan miji na bada kulawa ina ganin a zahiri zai fi kowa iya aiwatar da abin da ya rubuta, ita kuma burin mace daman samun mijin da ya san darajarta ne wannan kuma ina ganin marubuci na gaba-gaba wurin sanin darajar ‘ya mace.

Mujallar ADABI: Dakyau Malama Fatima, wannan amsa da kika bayar ta karkata hankalina zuwa kan muhawar da aka daɗe a na yi tsakanin al'umma inda ake samun wasu dake ganin marubuta na taka rawa ne wajen gyaran tarbiyya inda wasun kuma ke kallon akasin haka. Ko kin taɓa cin karo da irin wannan batu me kuma za ki ce a kai?

Fatima: Kusan shi ne ma kalubalen farko da na fara fuskanta a duniyar rubutu farkon fara rubutu na, na je islamiyya da littafin da nake rubutawa, wani labari, shugaban malaman mu ya karbe kuma yasa aka zane ni, kafin yasa wata malama ta min nasiha kan rubutu ba abu ne mai kyau ba, tun ina karama ta zan faɗa hanyar da ba daidai ba ce. 

Ni a waje na marubuci kan iya gyara tarbiyya haka ya kan iya batawa kuma kowanne aka ce marubuci n ayi ba a yi masa sharri ba gaskiya. Misali idan na dauki bata tarbiyyar da wasu marubutan ke yi na daukar dabi'ar rubuta batsa da shirme sai kama rasa shin wai sakon me suke son aikawa?

To a lokacin sai na ji na sare, sai dai kwarin gwiwar da na samu daga gida ne da suka tallafe ni. Ni a waje na marubuci kan iya gyara tarbiyya haka ya kan iya batawa kuma kowanne aka ce marubuci n ayi ba a yi masa sharri ba gaskiya. Misali idan na dauki bata tarbiyyar da wasu marubutan ke yi na daukar dabi'ar rubuta batsa da shirme sai kama rasa shin wai sakon me suke son aikawa? Kullum labarin daya ne shi ne rayuwar mata da miji na daki. To, ka ga wannan ba za a kira su da masu gyara ba sai masu batawa. Haka ta fuskar gyara tarbiyya, da yawan marubuta kan yi rubutu dan wayar da kan al'umma cikin nishadi ta inda za ka ga wani a da a na tayi masa nasiha ya kasa fahimta amma sanadin karanta kalmomin wani marubucin shi da kansa sai ya gyara. 


Wasu kan yi akan illar shaye-shaye, wasu illar rashin biyayya ga iyaye, wasu kan darajar ƴa mace da ba ta dama a rayuwa, wasu kan zawarci da matsalolin su, wani marubucin ko kiyasi ba ya sanyawa a labarin sa amma cikin hikimar da Allah ya ba shi sai ka ga an samu dubban mutane sun gyara kurakuransu.

Mujallar ADABI: Madallah. Shin kina da wani takamaiman lokaci da kika ajiye ne cikin zuciyarki ko buri da idan kika cika shi kike jin za ki daina rubutu?

Fatima: Gaskiya babu. Ban ma taɓa jin zan daina rubutu ba sai ma kullum burin na kara samun lokacin da zan rubuta wasu abubuwan da yanzu karancin lokaci yasa ban rubuta ba kasancewar makaranta tasa na rage yawan yin rubutun.

Mujallar ADABI: Shin mene ne babban burin ki a yanzu dangane da harkar rubutu?

Babban buri na shi ne abinda na rubuta ya isa ga jama'a su kuma fahimci sakon da na aika cikin labarin nawa.

Mujallar ADABI: wane saƙo kike da shi zuwa ga masoya masu karanta labaran ki?

Ina matuƙar godiya ga makarantan da suke bada lokacin su wurin karanta abinda na rubuta. Nagode.

Reactions
Close Menu