Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga masu ruwa da tsaki na Kannywood

 

Darakta Sunusi S. Bono

Ɗaya daga manyan daraktoci a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood ya aika da wani dogon rubutaccen saƙo dake magana akan takwarorinsa na masana'antar Kannywood wanda a bisa dukkan alamu wasu na yiwa sakon ganin wani abu ne da za ya ɓallo ruwa gami da sanya takaddama a tsakanin jaruman masana'antar da ake ganin tamkar sun zo wata gaɓa da ya rage saura ƙiris a kai ga ayyana su da zamowa tsintsiya madaurinki ɗaya. Ga abinda saƙon nasa ya ƙunsa kamar yadda ya rubuta.


Assalamu Alaikum jama'a zan ɗan yi wani sharhi akan wannan bawan Allah (Dauda Kahutu Rarara) dangane da irin sauya lissafin masana'antar shirya fina finai da yayi a lokacin da yan masana'antar da yawa suka yanke kauna da sana'ar a matsayin abinda zai riƙe su.

Dauda Adamu kahutu kowa yasan ba ɗan fim bane a farkon tasowar ɗaukakarsa, sannan kuma ba fim ne ya taimake shi gurin shahararsa ba, haka zalika babu wani ɗan film da zai ce shi ne yayi tallan DAUDA har duniya ta san shi ba, kuma ina da tabbacin idan bai jingina da fim ba kowanne irin buri nasa zai cika na ɓangaren layinsa na siyasa.

To amma me yasa ya zama garkuwa ga wannan masana'anta? Me yasa yake samo kudinsa a harkarsa ta siyasa da gwamnati ya kawowa cikin masana'antar? Amsa shi ne tausayi da karamci da kaunarsa ta tsamo yan masana'antar da ga cikin bakin talaucin da juyin juya hali da kura tsira da na bakin ki ya jefa masana'antar.

DAUDA shi ne ɗaya tilo daya fara karfafa gwiwar mawaƙa da makaɗa da 'yan rawa ta hanyar dawo musu da tunanin su jikinsu game da sana'ar da suke wanda a da sunfara yanke kauna da ita. DAUDA shi ne wanda ya fara saka kowacce irin gasa domin amfani da wannan damar gurin tallafawa 'yan masana'antar tare da saka kyautuka kala kala wanda haka ya saka wasu suka gani suka kwaikwaya wanda a yau duk wanda ya samu irin wannan farin cikin yana da lada na sunnanta kyakyawan aiki,

DAUDA shi ne wanda ya nunawa yan masana'antar cewa su shiga siyasa sukuma zama masu amfani da baiwar da Allah ya ba su ta kirkira domin zama tare da gwamnati don cimma manufa ta taimakon masana'antar wanda hakan yai sanadin dayawa suka samu damammaki a gwamnatance daga jahohi har Birnin tarayya Abuja DAUDA shi ne mutum na farko ɗan cikin masana'antar da ya fara empowerment ta hanyar bayar da ababen hawa kama daga MOTA BABUR DA KEKE NAPEP dasauran su ba don komai ba sai don karfafa gwiwa ta matasa dake masan'antar

DAUDA shi ne wanda ya fara yunkuri na tunawa da tsoffin yan masana'antar wanda duniya ta manta da su ta hanyar tallafa musu lokuta daban daban tare da kirkirar wasu ayyuka su don wanda ba zasu amfane shi ba amma yake yin su don su su amfana.

Kafin na bada misalai inaso mai karatu ya sani ban yi wannan rubutu domin wasu ba musamman yadda yanayi ya zama a cikin wannan masana'anta duk wanda yayi wani abu don taimakon yan uwanmu hakika abin farin ciki ne kuma cigaba ne amma inaso kusan yabon gwani yazama dole kuma da babu ɗan koyo da gwani ya ƙare kwana kwanan nan kamfanin RARARA MULTIMEDIA ya fito da wani tsari na yin fina-finai wanda za a gayyace yawa yawan wadanda ba a tafiya da su acikin masana'antar ko don zamani ko kuma don karin maganar nan da ake cewa SARKI GOMA ZAMANI GOMA wannan yunkuri an yi shi duk don farfado da masana'antar tare da wadannan jarumai kuma aka saka miliyoyin kuɗaɗe wanda na tabbata a yanzu babu kasuwar dawo da wannan kudi amma haka aka zuba su don kawai a farfafo da masana'antar daga suman da tayi.

Mu na addu'ar Allah ya taimaki wannan bawan Allah mai tsananin basira da kirkirar hanyoyi na motsa mana masana'antar da yasa wasu da su ka samu dama suma suke kokarin kwatawa dama wanda babu damar amma suke fatan idan sun samu zasu yi irin tasa Allah ya zaunar da kasarmu lfy da jahar mu ta AREWA da kuma masana'antarmu mai taken KANNYWOOD.


Nagode

AMINU S BONO

Reactions
Close Menu