Buduri a Kannywood: Ɗaya daga fitattun jarumai yayi kwanton ɓaunar yin wuf da Makama

Sunan Haruna Talle Maifata ba baƙo ba ne ga ma'abota kallon fina-finan Hausa, kodayake jarumin ya rage fitowa a finafinai yanzu idan aka kwatanta da shekarun baya lokacin da guguwar shuhura ke ingiza taurarinsa sama, fitaccen ɗan wasan dai a yanzu wanda ya kasance haifaffen Jos kuma ɗaya daga shugabannin kamfanin Maifata Films Production ya gama shirin sa tsaf don shiga daga ciki inda muka rasa gane wuf aka yi da shi ko shi ne yayi wuf da amaryar ta sa wato Zainab Dahiru wadda ake wa laƙabi da Makama.

Ɗaurin auren nasu wanda ake sa ran yiwuwarsa ranar Asabar mai zuwa cikin yardar Ubangiji wato ranar 12 ga watan Yunin 2021 zai wakana ne a unguwar Yakasai Gyanawa, Gidan Malamai dake garin Kano.


Ashe kuwa ranar Asabar idan Allah ya kai mu, za a sha buduri a Kannywood.

Reactions
Close Menu