Gajeren Ƙagaggen Labari: Bahagon Tunani


BAHAGON TUNANI

Na 

Abba Abubakar Yakubu


Misalin ƙarfe tara da rabi ne na dare. Ita kaɗai ce kwance a tafkeken gadon da ya cike kusan rabin ɗakin. Duhu ya mamaye ɗakin sai ɗan hasken da yake ratso ɗakin ta tsakanin labule mai haske da tagar uwar ɗakin ta. Da alamun hasken na fitowa ne daga ƙwan lantarkin da aka sa a tsakar gidan wanda kai tsaye yake kallon tagar ɗakin ta.


Farida na riƙe da waya a hannun ta tana hira da tsohon saurayinta Bala, wanda suka daɗe suna soyayya da shi, amma iyayen ta suka ƙi yarda ya aure ta saboda ba su gamsu da halayen sa ba, kuma ba a tabbatar da sana'ar da yake yi ba. Ba a son ranta ta auri Alhaji Sani ba, wanda a halin yanzu auren su bai wuce wata ɗaya ba.


Alhaji Sani Maiturare, babban ɗan kasuwa ne da ke da arziƙi daidai gwargwado, kuma mutumin kirki ne mai taimakon talakawa da riƙo da addini. Yana da mata ɗaya mai suna Hajiya Binta da yara mata guda uku. Allah ya jarabce shi da son Farida tun a lokacin da ya fara ganinta a wajen saukar karatu na makarantar Tahafizul Ƙur'an, inda aka yaye ɗaliban da suka yi sauka.


Ya so ta saboda kyan surar ta da kuma natsuwar da ya gani a fuskar ta. Da gani za ka san ta fito ne daga gidan tarbiyya. Amma abin da bai sani ba shi ne Farida yarinya ce mai buɗaɗɗen ido da son 'yan garanci, duk kuwa da ƙoƙarin da iyayen ta suke yi a kanta na bata tarbiyyar addini yadda ya kamata.


Bala, saurayin da Farida ta yi a layin da take zuwa makaranta shi ya fara sanadin buɗewar idanun ta, da sanya ta a harkar shaye shaye da zinace zinace, ba da sanin iyayen ta ba. Kuma ko da aka hana ta auren sa, ba ta yarda sun rabu ba. Ta ci gaba da mu'amala da shi ta waya, suna kuma shirin cigaba da harkar da suka saba, ta rashin tarbiyya. Amma aure ya mata cikas, domin ba ta samun fita. Bilhasali ma tun da ta yi aure sau ɗaya ta fita zuwa gidan su, shi ɗin ma tare da mijin ta suka fita a mota.


Ta juya ta kalli gefen da mijinta ya saba kwanciya, wajen na nan fayau a gyare ba kowa, tun da yau ba kwanan ta ba ne. Ta yi tsaki, a ranta kuma ta ji wani farin ciki ya ratsa ta. Duk ranar da mijinta ke ɗakin ta ba ƙaramin ɓacin rai take ciki ba, saboda yadda ta tsani ta ganshi kwance a kusa da ita. Babu ma kamar a ce idan ya buƙaci saduwa da ita, sai ta ji kamar ta haɗiyi rai ta mutu.


Ta yi ajiyar zuciya, yayin da ta tuna yadda suke soyayya da Bala, wanda shi ya fara ɗauke mata budurci, kuma ya koya mata duk wani salo na saduwa tsakanin mace da namiji. Babu namijin da take so a duniya in ba shi ba.


"Gaskiya ni fa na gaji da zaman gidan nan, yadda ka san a kurkuku nake ko a cikin wuta." Ta rubuta a hirar da suke yi ta manhajar WhatsApp.


"Ni ai na fi ki damuwa, kamar na yi tsuntsu na zo inda ki ke..."


"Ina tsananin buƙatar ka kusa da ni. Wai har yanzu ba ka samo mana mafita ba ne?"


"Hanya ɗaya ce nake tunani a kan ta, ban san ko za ki amince da ita ba..."


"Wacce shawara ce?"


"Sace ki zan yi, in yi garkuwa da ke, in sa mijinki ya biya kuɗin fansa, sai mu gudu tare, mu je inda za mu zauna mu yi rayuwar mu hankali kwance!"


Ta yi ajiyar zuciya


"Amma fa ka yi tunani, ni hankalina bai ma kai can ba... Yaushe za ka sace ni?"


Tana rubutun gabanta na faɗuwa, amma kuma a ranta tana tunanin hakan ce kawai mafita na yadda za ta samu 'yanci daga auren dolen da aka yi mata.


"Shiryawa za ki yi kamar za ki je anguwa, sai in turo miki mai A Daidaita da zai ɗauke ki a bakin layinku, ya kawo ki inda nake a bayan gari, ta yadda za mu kaucewa sa'idawa."


Ta gyara kwanciyar ta, tare da yin wani ɗan murmushi a furkar ta, "An gama, baby." Kamar yadda ta saba kiran sa.


***** ***** *****


Ƙamshin turaren Alhaji ne ya fara dukar hancinta, yayin da ta ɗago kai daga kwanciyar da take yi, ta dubi ƙofar shigowa uwar ɗakin ta.


"Salamu Alaikum," in ji Alhaji Sani


Yana sanye da babbar riga, 'yar ciki da wando na farar shadda wagambari ta sha sitati, kansa da hula Zanna Bukar da baƙin takalmi sau ciki, a ƙafarsa.


Ta amsa a sanyaye ciki-ciki, "Wa Alaikumus Salam"


Ya ƙaraso kusa da gadon da take kwance, "Amarya, lafiya kuwa har yanzu kina kwance ko falo ba ki fito mun gaisa ba?"


Muryar sa da alamun nuna damuwa


Ta yunƙura ta tashi zaune a marairaice, "Wallahi tun jiya ban runtsa ba, cikina na azabar ciwo, mara ta a ɗaure, da ƙyar na shiga bayan gida na yi alwala."


"Subhanallah, shi ne ba ki kira ni a waya ba, ko ki taso yayar taki?"


Cikin murya mai shagwaɓa, "Ni ba zan kira ka kana wajen Aunty ba, ai sai ta yi zargin wani abu."


"Zargin mai za ta yi, ba lalura ba ce? Tashi za ki yi ki shirya ki je asibiti, yayar taki ta raka ki."


Ta ci gaba da langwaɓewa tana cewa, "A'a ba sai na ba ta wahala ba, na kira Samira ƙanwata za ta raka ni."


Alhaji ya sa hannu a aljihu ya fito da wasu kuɗaɗe ya ƙirga dubu biyar ya miƙa mata. "Ga wannan ki riƙe a hannu ku je asibitin, zan kira ki in ji yadda ku ka yi."


***** ***** *****


Fitar Alhaji Sani ke da wuya sai Farida ta tashi zumbur tashi ta kira Bala, ta gaya masa cewa komai ya yi daidai, sannan ta shiga wanka. Dama tuni ta gama shirya kayan da take so ta fita da su. 


Tana kammala shiryawa, sai ta kira Bala, wanda ya yi mata bayanin yadda za ta gane mai A Daidaitan da ya turo mata, ya kuma gaya mata ta kula da kyau kada wani ya yi zargin wani abu tare da ita.


Farida ta ɗauki ƙaramar jakar da ta shirya kayanta a ciki, sannan ta ɗauki ƙaton hijabi, ta saka a kanta tare da ɗaura ƙyallen niƙabi da ya ƙara rufe fuskar ta.


Cikin zumuɗi da saurin fita kafin wani ya ankara da fitar ta, ta manta da babbar wayar da take amfani da ita a ɓoye tana shiga zaurukan sada zumunta tana hira da saurayinta.


***** ****** ******


Ƙarar wayar sa ce ta katse masa hirar da yake yi da abokin sa da ya kawo masa ziyara har ofishin sa.


"Hello."


Wata murya mai tsoratarwa ta ƙara sa shi cikin natsuwa.


"Matarka Farida tana hannun mu, mun sace ta. Ka nemo mana kuɗin fansa Naira miliyan goma sha biyar, nan da awa arba'in da takwas. Za mu kira ka mu sanar da kai yadda za ka bayar da kuɗin, amma kafin nan muna gargaɗin ka ka kiyaye, kada ka kuskura ka sanar da jami’an tsaro ko wata hukuma. Za mu kashe matarka, kuma mu biyo ka har gida mu kashe ka. Ka yi wa kan ka ƙiyamullaili!!! "


Gaban Alhaji Sani ya faɗi, hankalinsa ya tashi.


"Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un!"


***** ****** ******


A cikin sanyin jiki ya shiga ɗakin amaryar sa, zuciyar sa cike da fargaba da jimamin halin da take ciki. Bai san mai zai gaya wa matar sa Binta ba, saboda gargaɗin da aka yi masa. Ya kamata yau a ɗakin ta zai kwana.


Kamar an ce kai hannu can, sai ya kai hannu ya jawo dirowar gefen gadonta, sai kuwa ya ga wayar matarsa. Ya ɗauka yana jujjuya ta, hankalinsa bai kai kan ya buɗe ba, don tunanin ko a kulle take. Amma ga mamakin sa, sai ya ga yana ɗora hannu ta buɗe, kai tsaye sai hannun sa ya kai kan WhatsApp ɗin da ke kan wayar.


Zumbur ya miƙe tsaye, cikin mamakin abin da idanun sa suka gani, irin hirarrakin da suke yi da tsohon saurayinta Bala.


Kai duniya!!!

Reactions
Close Menu