Gwarzuwar Aminiya: Shin wace ce Rufaida Umar?Wannan kammalallen rahoton da wakilin mu ya hada mana ne na rubutaccen tarihin gwarzuwar gasar Aminiya Trust 2020, Rufaida Umar Ibrahim wanda ta rubutowa Mujallar ADABI da hanunta. Hakan ya faru ne biyo bayan nasarorin da marubuciyar ta samu sau biyu a shekara guda cikin manyan gasannin rubutun kagaggun labarai wanda yasa muka yi ta samun sakonnin masu sha'awar son ganin mun tattauna da marubuciyar don su san tarihin rayuwarta.


Wace ce Rufaida?

Rufaida Umar Ibrahim shi ne cikakken sunanta. Mahaifinta ya kasance ɗan asalin garin Kano ne, ita kuma mahaifiyarta asalinta ƴar garin Diffa ce dake kasar jamhuriyar Nijar. Ta taso a cikin kauna da kuma gata irin ta kulawa daga wurin iyayenta da kuma ‘yan uwan ta.


Mataki Da Rayuwar Karatunta:

Rufaida ta kammala karatunta na firamare ne a shekarar 2005, wanda hakan ya ba ta damar kamala karatunta na sakandire a shekarar 2011. Sai dai duk da kasancewar ta samu kyakkyawan sakamako a manyan jarrabawarta na karshe yayin kammala sakandiren, wato WAEC da NECO. A lokacin Allah bai ƙaddara za ta ci gaba da karatun nata ba duk kuwa da irin burin da ta ci akan haka, amma a yanzu haka tana kan cigaba da karatun cikin hukunci na Ubangiji, inda take aji biyu a kwalejin horar da malamai wato FCE dake garin Kano. Rufaida a yanzu haka tana karantar ilimin nazarin halittu ne hade da kimiyya (Biology/Integrated Science), sosai take kaunar ɓangaren da nake karanta amma jama'a da dama na ba ta shawarar ta sauya ɓangaren karatun nata don a cewar su ba da nan ta dace ba, a ganin su za ta fi dacewa ne da aikin jarida ko gidan rediyo. 

Rufaida sam ba ta fiye mamakin jin irin hakan ba, domin ko ba komai tana da tabbacin cewa su na duba ne da irin baiwa ta fasahar ƙirƙira da Allah Ya ba ta matsayinta na marubuciyar da daidai gwargwado mutane da dama suka san ta. Sannan kuma ga karance-karancen labaran ta da suke yi a kafafen sadarwar sada zumunta na intanet kamar su Whatsapp, Facebook, Wattpad da sauransu. Ita kan ta takan yi alfahari da irin baiwar da Allah Ya ba ta, kuma a koyaushe tana cikin godiya a gare Shi.


Yadda Ta Fara Rubutun Labarai:

Rufaida tun tana sakandire ta taso da ƙauna da soyayyar rubutu a dalilin yawan karance-karancen litattafan Hausa. Ta tabbatarwa Mujallar ADABI cewa ba ta mantawa da lokacin da ta fara gwada rubutu a takarda, a lokacin takan yi ne ta ajiye ba don tana da tabbacin daidai take yi ko kuma ba daidai ba. A cikin hakan ne watarana daya daga yayunta ta ce mata ta karanta rubutun da tayi kuma ya yi mata dadi sosai, ta ci gaba. Jin hakan yasa mamaki da farin ciki ya kama ta, a sannan ne kuma sai ta ƙara fahimtar cewa lallai za ta iya idan har ta ƙara dagewa. Cikin ikon Allah bayan fara hawa whatsapp da tayi, ta fara gwadawa, da kadan-kadan sai ga shi sunan Rufaida Umar ya zama daya daga cikin na masu rubutu online. Yawan Rubuce-Rubucenta:

Rufaida zuwa yanzu dai ta rubuta labarai sama da goma sha biyar, cikinsu akwai Mahaifiya, ‘Yar Bariki, Rayuwa Ce, Rayuwar Hamida, Dan Adam, Mijin Mace Daya, Ƙarfen Ƙafa da sauran su.


Lambobin Yabo Da Nasarorinta:

Rufaida ta fara samun shaidar  karramawa karo na farko a harkar rubutu ne daga kungiyar HAF, inda suka ba ta shaidar karramawa ta musamman a matsayinta na marubuciya. Ta kuma taba samun gayyata daga ANA a matsayin baƙuwa ta musamman, inda na amsa tambayoyin jama’a da dama game da rubutu. A shekarar 2020 tayi nasarar zamowa gwarzuwa ta uku a gasar BBC HIKAYATA. A cikin kuma dai shekarar ta kara yin wata nasarar a matsayin gwarzuwa ta ɗaya a gasar farko ta AMINIYA TRUST. Burinta Zuwa Gaba:

Rufaida dukda haka na da buri da kuma fatan ganin zuwan wasu nasarorin da suka fi haka a nan gaba. “Zan iya cewa rubutu ya yimin komai, ba kuma zan gaji da kaifafa alƙalamina ba da yardar Allah.”

Reactions
Close Menu