SABUWAR MUƘALA: HAUSA BA DABO BA CE

------------------------------------------------------ 

Daga Aliyu Umar Yaro

auyarom@gmail.com 

-------------------------------------------------------- Wannan rubutu zai yi magana ne akan mece ce Hausa? Ci gaban harshen Hausa a duniya, sai kuma cikas/ tirjiya -Allah ya sauke- da Hausa ke fuskanta. A kokarin fayyace mece ce Hausa zai yi kyau mu kawo ra'ayoyi/binciken masana dangane da abubuwan suka fada ko rubuta akan shahararen harshenmu na Hausa. 

RA'AYIN MASANA 

SCHUH (1983) Hausa daya ne daga cikin manyan harsunan na duniya, wanda in ban da Larabci, babu wani harshe da ya fi shi yawan jama'a a nahiyar Afrika. 

GREEN BERG (1947) Harshen Hausa yana daga cikin kungiyoyin harshen Chadi, don haka yake da dangantaka da harsuna irin su: Masa, Lasa, Sokoro, Kotoko, Kera, Tera, Bura, Margi, Mandara, Balanci, Warji, Karekaranci da Sauransu. 

CI GABAN HARSHEN HAUSA

Allahamdu lillahi, kamar kashen Turai, Asiya, Amirka sun jima suna amfani da Hausa. Sannnan Jami'o'i a Afrika da Turai da Amirka da wani Sashe na Asiya sun jima suna koyar da kwasa-kwasai samun digiri na farko, digiri na biyu, kai har ma fa da digiri na uku akan Hausa. Har wala yau, in ban da Larabci babu wani harshe a Afrika da yake da kamus mai girma da yawan kalmomin kamar kamus din Hausa wanda wani Bature mai suna Bergery (1934) ya rubuta; wannan kamus yana da kalma guda dubu arba'in da tara+ (49,000+)

CIKAS KO KALU BALE - ALLAH YA SAUWAKE- DA HAUSA KE FUSKANTA

Duk da irin Wannan ci gaba da bunkasa da Hausa ta samu a duniya, babban abin takaicin shi ne har yanzu Hausa ba ta zama harshen wata kasa ba! Ma'ana harshen da wata kasa ta dauka a matsayin harshen al'amuran ilimi da kimiyya da fasaha da siyasa da sauran bangarori na gwannati. San nan abin kule ga Hausawa shi ne ' Turawa ne suka yi ma fi yawan nazarce-nazarce akan harshen Hausa, kuma har yanzu ma fi yawan rubuce-rubuce kan harshen Hausa da Ingilishi aka yi!. 

---------------------------------------------------------- 

A.U YARO

+2348144321344

auyarom@gmail.com

Reactions
Close Menu