Gajeren Labari: 'Jiki Magayi' na Hassana Abdullahi Hunkuyi

  

JIKI MAGAYI

****

Na

****

HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI


“Wayyo! Allah, babana ka zo ka cece ni,  Mama zata kashe...” Salma ba ta ida maganar ba, ta sake jin fas! Tas!! Kau!!! A dukkan kuncinta. Gambo ta fara magana cikin ɓacin rai, “Na lura kinfi son ubanki a kaina, me yasa kika ba shi kuɗina? Daga yau kya kuma kiran mai alewa ba ki da kuɗi.”

Ta ci gaba da laftar Salma kamar ba ita ta kawo ta duniyar ba. Salma tana kuka take faɗin, "Wallahi ɗari biyun faɗi ta yi." Sharri!! Ta saki fitsari a tsaye sakamakon jin furucin da ƙaninta ya yi. "Mama, ina ganin lokacin da anty Salma ta ba babanmu kuɗin ta ce ya ci abinci." 

 A fusace Gambo ta wafci muciyar tukin tuwo  zata ɗirka mata,  amma ta ji an riƙe muciyar ta baya. Kafin ta waiga ta ji saukan duka a gadon bayanta. Ba ta yi sanya ba, ta rarimo tukunya mai ƙafa ta durfafi mijinta, cikin gagarumar sa'a ya goce. Nan dai  Suka yi kare jini biri jini.

*****

 Uzairu, irin mazan nan ne marasa son moriya. Tun fil azal, matacciyar zuciya yake da ita.  Bai san komai ba banda ya ci, ya sha, ya saka mai kyau, soyayyar Gambo ta sangarta shi,  baya cas! baya as! Domin ta riƙe masa kan maciji yana wasa da shi yadda ya so.

Gambo, mace ce mai son neman na kanta, duk wani abu da za a sana'anta a sami riba tana yinsa. A haka suka tara zuri'a tare da Uzairu. Komai na gidan, karatun yara, cinsu, shansu, da sutura, duk Gambo ke yi, hatta kuɗin kashewa  Uzairu baya fatararsu. Har abokansa na yi masa laƙabi da, dan gatan matarsa.

Kwatsam! Aka yi wa Uzairu alƙawarin ba shi aikin gwamnati, amma sai ya kai wasu maƙudan kuɗaɗe.  Gambo, ta yi iya yinta don ta hana shi kai  wannan kuɗi amma sai ya kada baki ya ce mata, "Na lura kina jin tsoron rashin samun nasara ne ko? Idan na ƙi  yin kasada, ban cika jarumi ba, shi kuwa jarumi baya tsoron yin asara, domin rashin nasara wata matakala ce na daukaka."

Bayan Uzairu ya kai kuɗi an cinye, sai aka fara wasan kulli kurciya da shi da masu kuɗin daya basa. Ita kuma  Gambo ta tsuke bakin aljihunta, amma da taga wankin hula na neman kai mijinta dare sai ta dauki kuɗin kan dole ta biya masa bashin. Hakan bai dakusar da sha'awar Uzairu na son aikin gwamnati ba, kullum cikin fangan-fangan yake yi tsakanin kamfanoni da ma'aikatun gwamnati.

Ran nan aka kirata a kyauye ana mata murnar ta biya aikin hajji, Gambo ta buga ƙirji, "Goggo, ina naga kuɗin zuwa Saudiyya? Ƴan sana'aoin nawa basu taka kara sun karya ba. Amma waye ya faɗa maku?"

Gogga ta ce, "Uzairu ya zo ya faɗa mana zai biya maki aikin hajji amma kuɗin ba su cika ba, shi ne kika ce azo a siyar da buhunan barkonunki duka, sannan a  haɗa da shanun da ƙaninki ke  huɗa dasu a siyar.

Nan ta ke aka kai komai kasuwa aka siyar, da ya ƙirga kuɗin sai ya ce ba zasu kai ba, don haka na haɗa masa da tumakinki da ake kiwo, shi ne na kira ki yanzu  in yi maki murna haɗi da sanar da ke cewa gobe dangi za suyo mota guda su zo maki murna..." Gambo ta saki kuka, "Goggo, gani nan zuwa kauyen yanzu. Idan na zo zaki ji cikakken bayani."

 Gambo ta sami Uzairu a ɗaki yana duba wasu takardu. Ta kalle shi fuska cike da hawaye ta ce, "Uzairu, sakayyan da zaka yi min ke nan? Ni da zuciya ɗaya nake zaune da kai, amma kai na lura mugunta ce fal a ruhinka, to ka sani, jini baya maganin wuta, kamar yadda haram baya kashe ƙishi, na daɗe da sanin irin ɓarna da kake yi min, na ji abin da kaje kyauye kayi."  Uzairu ya kada baki ya ce, "Na ranci kuɗin ne na kai za a samar min aikin gwamnati, in ba hakan nayi maki ba, ba zaki ranta min kuɗin ba, ki sha kuruminki duk ranar dana sami aikin, zan biyaki kuɗaɗen ki. 

Uzairu bai dandara ba, sai ya sake wata sabuwar dabarar, duk inda ya san ana mutunci da Gambo, sai yaje ya ranci kuɗi da sunanta. Hatta gidan da Gambo ke kai adashi, ya tura  ɗiyarsa Salma taje ta amso kwasa a matsayin Gambo ce ta aiko ta.

Ya zuwa yanzu kowa ya san halin Uzairu, dangi gaba ɗaya kaf suka juya masa baya. Musamman da suka ga ya naƙasar da Gambo, komai nata ya kare, jarinta ya rushe ta dawo bata da komai banda yara cima zaune.

Tun daga wannan lokaci Gambo, ta daina tausayin Mijinta, ta kuma tsani ɗabi'unsa. Idan wani abu nata yaje hannunsa ko yara suka bashi sai sun ci kafirin duka, kamar dai dukan da Salma ta sha,  don ta ba babanta naira dari biyun da aka aike ta ya ci abinci.

Bayan kwana biyu,  Gambo ta gabatar wa Uzairu da  kudirinta na son rabuwa da shi muddin bai rumgumi sana'a ya bar maitan son aikin gwamnati ba. Uzairu ya harareta ya ce, "Duk bakin cikin tanda sai na ci waina, ko ana ha! Maza ha! Mata sai nayi aikin gwamnati sai dai ki ɗauki mataki."

Uzairu ya lura, matakin da Gambo ke son ɗauka ba zai haife masa ɗa mai ido ba, don haka ya sakko daga tsanar ƙin yin sana'ar hannu. Ya roƙi matarsa gafara haɗi da rumgumar sana'ar hannu, yaransa kowane ya kaishi wajen koyon sana'a. Kafin wani lokaci liyafarsu ta ci gaba. Sai yanzu yake jin haushi kansa da tuntuni ya ƙi rumgumar sana'ar hannu.

Gambo ta kalleshi a kaikaice tace, "Na ji za'a ɗauki ma'aikatan gwamnati, ko zaka gwada sa'ar ka?"

Ya aje kuɗin da yake ƙirgawa haɗi da harararta, "Aikin gwamnati na mai matacciyar zuciya ne, Ni kam!, zuciyata bata mutu ba." Gambo ta kyalkyale da dariya, "Ka da ka faɗi haka Abu Salma, aikin gwamnati abu ne mai armashi  idan mutum ya haɗa da sana'a."

Reactions
Close Menu