Karanta Littafin 'Shaheed Na Shaheedah' Shafi na 1

Shaheed Na shaheedah 4.1k

SHAHEED NA SHAHEEDAH (Shafi na 01)

Marubuci: Abdul-azeez Shehu (Yareema Shaheed)

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ

      Misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranan Asabar, garin ya ɗan yi duhu sakamakon hadarin da ya fara tasowa, wata sassanyar iska ke kaɗawa a hankali wanda ya yi sanadiyar kaɗawan bishiyoyi da furanni da ke shuke a wajajen, hakan ba ƙaramin taimakawa ya yi ba wajen bayar da walwala da annushuwa ga al'ummar yankin, da alamun kowa na jin daɗin yanayin sanyin daminan, a hankali ido na ya fara hango min wani katafaren gidan sarauta, wanda gabaɗaya ya ja hankalina don ban taɓa gani ko jin labarin gini mai kyau da ƙayatarwa da tsaruwar wannan gidan sarautar ba.

         Duk da tsarin ginin ya kai girman gari guda, amma hakan bai sani jin tsoron ƙin zuwa gidan ba, don ina son ba ma ido na abinci, na shiga cikin gidan na yi kallo.

      Na daɗe kusa da babban ƙofar Masarautar wanda shi ne zai kai ka ƙofar shiga cikin gidan sarautar, ɗaga kai na, na yi naga an rubuta.

 *MASARAUTAR AFRANA* , har yanzu tunanin yadda zan yi na samu damar shiga gidan sarautar nake yi, wasu manyan Dogarawa ne masu tsaron ƙofar gidan sarautar, sun sanya babban riga kalan kore da ratsin ja da jan rawani, hannunsu ɗauke da manyan bulalai wasu na ɗauke da bindiga wasu na riƙe da kwari da baka, fuskar su a ɗaure babu alamun wasa a tare da su, har yanzu tunanin ya za ayi na samu dabarar da masu tsaron gidan za su barni na shiga ciki na yi kallo nake, lallausar murmushi ne ya bayyana a labɓana lokacin da na hango wata tawagar sanye da irin tufafin da ke jikina sun tunkaro ƙofar shiga cikin fadan ba tare da ɓata lokaci ba na yi wuf! Na shige cikinsu.

        Tawagar farko mutane ne masu manyan riguna masu layi-layin na kore da ja da rawani kalar ja, da alama Dogarai ne.

        Bayan su wasu 'yan mata ne kyawawa sun sa riga da zani mai ruwan shuɗi iri ɗaya, tafe suke su na rera waka mai daɗin ji a kunnan mai sauraro.

      Bayan su kuwa wasu Hadimai ne su huɗu su ke ɗauke da wani ƙayataccen tantin rumfa abun ɗaukan mutane irin na gidan sarauta, amma ba na hango abin da ke cikin tantin, take zuciyata ta ƙaramun ƙarfin gwiwar lallai sai na ga abin da suka ɗauko a cikin wannan abin mai kama da ɗaki ko rumfa.

     Nan da nan na bi bayan Dogarawan da ke biye da Hadimai masu ɗauke da wannan tantin rumfa na shige tsakiyarsu.

      Muna isa ƙofar shiga gidan sarautar aka wangale shi muka fara shiga ciki, muna shiga na saki baki ina kallon ikon Allah. Domin fadar ta yi kyau da tsaruwa abin sai wanda ya gani.

     Ƙaton fili ne mai cike da shuke-shuken furanni masu kyau da ƙamshi, sannan ga Dogarawa an sasu a lungu da saƙon cikin gidan sarautar, ba daman ka yi wani wargi, ni dai sunkuyar da kaina na yi dan tsoro ina tambayar kaina me ya sa na kawo kai na, wata zuciyar ta ce mun "Tsegumi."

      Cigaba da bin su na yi, har muka kawo wani tsararren gini mai matuƙar tsaruwa an yi masa kwalliyar zanen sarauta mai ɗauke da kalar ja,baƙi,kore da ruwan kwai, haka na ci gaba da binsu har wajen ƙofar shiga ɗakin , a daidai nan ne Dogarawan farko suka ja birki suka tsaya, sai wani guda ɗaya ne ya ci gaba da binsu har bakin wani ƙofa, nan wasu Dogarai masu gadin ƙofar suka zube suna miƙa gaisuwa faɗi suke "Barka da dawowa Gimbiya 'yar Sarki jikar Sarki, hutawarki lafiya sarauniyar kyawawa, Allah ya ja zamaninki ranki shi daɗe."

    Wani Hadimi ne ke amsa gaisuwar da Dogarawan ke ma Gimbiya, faɗi yake, "Gimbiya ta amsa."

    Daga nan ya dawo bayan wajen Hadiman nan wanda suke ɗauke da tantin rumfa ya yi musu nuni da hannu, nan take suka duƙa tare da sauke tantin rumfar a hankali, sai biyu daga cikin 'yan matan nan suka buɗe labulayen tare da cewa,

    "Allah ya baki yawan rai! Ranki shi daɗe mun iso gida, umarnin ki muke jira mu shiga cikin Turakar ki Ranki shi daɗe."

         Bayan kimanin wasu 'yan mintunan da ba zai wuce biyar ba, sai ga wani santalelen hannu ya fito daga tantin rumfar, nan take wata daga cikin 'yan matan nan ta kama mata hannu a ladabce ta ce, "Godiya nake ranki shi daɗe."

       Ban tsinke da lamarin ba sai da na hango wata matashiyar budurwa mai shiga ta alfarma, ta fito cikin tantin rumfar, sanye take da Alkyabba mai ruwan madara an mata aiki da kalar ruwan gwal, hannunta sanye da wasu zobuna na gwal guda biyu, duk yadda naso ganin fuskarta abin ya gagara sakamakon rufe fuskarta da ta yi da hular Alkyabbar.

     A haka ta fara takawa a hankali har cikin gidan, Hadimai mata na biye da ita huɗu ta gaba, bakwai ta baya.

     Sai sauran Dogarawan da suka tsaya a bakin ƙofa da alamun ba za su bisu cikin Turakar ba.

   Ni dai haka na ƙutsa na bisu cikin Turakar, muna shiga na yi arba da wani ƙayataccen falo mai ɗauke da kayan alfarmar sarauta, falon na ɗauke da kumbo da furanni tare da kwalliyar gashin ɗawisu an mannasu a jikin bangon falon. 

    A ɗayan gefen kuma wata lallausar shimfiɗa ce ta alfarma mai ɗauke da kilisai masu taushi, a hankali Gimbiya ta isa wajen shimfiɗar kilisan ta zauna tare da kishingiɗa da wani babban tuntum, Hadima Lamira ce ta zo ta gyara mata Alkebbar tare da cewa , "Zauna daidai Gimbiya, hutawarki lafiya Uwar gijiyata." Lamira ta ci gaba da magana ta ce, "Ranki shi daɗe, na sa Madugu ya kawo miki madara irin wanda kike matuƙar so a irin wannan lokacin ranki shi daɗe." 

   Girgizar kai Gimbiya ta yi ba tare da ta ce komai ba, Lamira miƙewa ta yi tare da cewa godiya nake ranki shi daɗe Uwar ɗakina. 

        Ɗauko wani babban faranti Lamira ta yi mai ɗauke da kayan marmari kama daga su abarba,ayaba,lemon zaƙi,tufa da dai sauransu, sa hannu ta yi ta ɗauko ayaba guda ɗaya ta ɓare, sannan ta miƙawa Gimbiya tare da cewa, "Ga wannan ki ɗan taɓa Uwar ɗakina."

        Gimbiya ɗaga hannu ta yi tare da nuna alamar ba ta buƙata....cikin ladabi Lamira ta ce, "Tuba na ke ranki shi daɗe." Ta shi ta yi ta je ta ajiye ayabar.

    Hakan ya yi daidai da shigowar wani matashin saurayi mai ɗauke da wata ƙwarya wanda aka yi mata zane mai ban sha'awa a hannunsa, sanye ya ke da riga 'yar shara da wando fari da rawani kalar shuɗi, bakwa iya ganin fuskar sa, domin ya rufe fuskar shi da rawanin dake kansa illa idanunsa zaku iya gani, bayan ya yi sallama Hadima Lamira ta amsa mishi gaisuwar, kusa da Gimbiya ya je ya duƙa, cikin ladabi tare da sassanyar muryar shi mai daɗi ya gaishe ta tare da cewa, "Tuba nake yi ranki shi daɗe, ban ɗauka zaku dawo yanzu ba, kuma nasan baki son madarar da ta daɗe da tatsa, shi yasa na yi jinkiri, ki gafarceni ranki shi daɗe."

     Gimbiya shiru ta yi, ba ta yi magana ba haka bata ɗaga kanta ta kalle shi ba, shi ko Madugu a take jikin shi ya fara rawan ɗari, duƙa kan shi ƙasa ya yi cikin tsoro ya ƙara tuba a gabanta, Gimbiya gajiya ta yi da jin Madugu dan ya cika mata dodon kunne da magana, ita kuma ba son hayaniya take ba, don haka ta ɗaga mishi hannu alamar ya isa, ya tashi ya tafi.

      Godiya Madugu ya yi tare da miƙewa dan shirin tafiya, tun da ya gama aikin sa, miƙewar da zai yi kawai hannun shi ta bigi gefen ƙwaryar kawai be yi aune ba sai gani ya yi ƙwaryar ta tuntsure, madaran na ta malala a ƙasa, kan ya yi wani yunƙuri har madarar ta isa gurin Gimbiya ta ɓata mata kayan jikinta.

      Cikin tsoro da damuwa Madugu ya zube ƙasa, yana neman gafarar Gimbiya Rameesah dan yasan yau babu mai cetonsa wajen Gimbiya Rameesah sai Allah.

      Gimbiya Rameesah ta kasance ko kaɗan ba ta ɗaukar raini ko wargi, shi yasa kusan kowa a gidan sarautar ke shayin shiga hurumin ta.

       A hankali Gimbiya Rameesah ta ɗaga kanta ta kalli inda madarar ya malala tare da jiƙa mata kayan ta, dawowa da kallon ta ta yi kan Madugu, a daidai lokacin Lamira ta cire ɗankwalin kanta dan goge inda madarar ya ɓata a jikin Gimbiya Rameesah, amma ina harara Gimbiya Rameesah ta bi Lamira da shi, don ganin zata sa mata ƙazamin ɗankwalinta a jiki, jikin da batason ko ƙuda ya taɓa shi sai dole.

       Sunkuyar da kai Lamira ta yi tare da faɗin, "Tuba nake ranki shi daɗe, raina fansane a gareki.

       Gimbiya Rameesah ba da umurni ta yi aka kira wasu Hadimai majiya ƙarfi, dama idan wani ya yi laifi cikin gidan su ake kira don su hukunta mai laifin.

       Bayan kamar minti ɗaya, Gimbiya Rameesah ta yi ajiyar numfashi cikin ɓacin rai ta ce, "Ku ɗauki wannan ƙazamin Madugu ku je ku kulle shi a cikin ɗakin duhu, kuma ku azabtar da shi, sannan gobe ku tara mutane ku yanke masa hannunsa na dama, domin ya gane kuskurensa, in yaso daga yau ba zai ƙara yin kuskuren zubamun wani abu a jikina ba."

    Cikin ladabi Madugu ya ce, " Ranki shi daɗe Tuba nake, kuma ina godiya da hukuncin da kika yanke mun ranki shi daɗe." Yana gama magana, ba tare da ɓata lokaci ba, aka tisa ƙeyar Madugu aka tafi da shi ɗakin duhu.

      Abin da ya ƙullema Hadiman gidan sarautar kai shi ne, yadda Madugu ya yi ma Gimbiya Rameesah godiya ba tare da ya nemi afuwa akan kar a yanke masa hannun ba, to me hakan ke nufi, ko dai shi Madugu bai damu da rayuwar shi ba ne, haka dai mutane ke ta ƙananun maganganu akan Madugu.

 Kash! laifin daɗi ƙarewa ku biyo ni domin jin cigaban labarin yadda zai kasance.

Za ku iya yin tsokaci da sharhi a sashen comment box din mu dake kasa.

Reactions
Close Menu