Kukan Kurciya (1): Son Zuciya, Ɓacin Zuciya

Daga Abba Abubakar Yakubu 

Ɗaya daga cikin halayen da ke zama ƙalubale ga cigaban zumunci da zamantakewa shi ne son kai. Mutane masu son kansu suna haifar da damuwa, ƙunci da ƙiyayya mai yawa, saboda sun fifita son zuciyarsu a kan amfanin da jama'a da dama za su samu. A kan abu ƙalilan da wani yake ƙwadayin samu sai ya rusa jin daɗin da ƙoƙarin da wasu suka daɗe yana yi.


Mun sha jin ƙorafe ƙorafe daga mutanen da aka tauye wa haƙƙi ko aka zalunta, sakamakon son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.


Akwai mutanen da za ka riƙa yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwaɗayin samun wata alfarma daga wajensu. Sai dai da a ce za ka samu jin abin da waɗanda ke ƙarkashin sa ko iyalinsa suke faɗa, ba za ka so ka sake kallon sa da martaba ba. Saboda halinsa na rashin fitar da haƙƙin waɗanda suka yi masa ƙwadago da gumin su, sauke nauyin iyali da 'yan uwa da ke kansa. Yana ganin idan ya cire wani abu daga arziƙin sa to, zai rage masa jin daɗi, ko zai bayar a inda ba a san zafin su ba.


Yana yi wa mutane wahala su sadaukar da wani ɗan yanki na jin daɗin su, walwala ko damar da suke da ita don wani ya amfana. Sai ka ga ana ta fama da wani a cikin motar haya kan ya ɗan gyara zamansa domin kowa ya ji daɗin zama, amma mirsisi sai ya ƙi, saboda tunanin idan kowa ya zauna da kyau shi ba zai sake yadda yake so ba. Haka ma ko a gaban ubangiji wajen sauke farali, za ka ga wani ya yi babakere a waje ana roƙon sa ya gyara zama ko tsayuwar cikin sahu, amma yana ganin za a takura masa shi ba zai yarda ba.


A duk yayin da mutane suka fahimci wane yana da halin rowa, son kai da rashin sassauci a harkokin rayuwar to, yana zama abin ƙyama da yi wa kaffa kaffa. Kyautatawa da nuna halin kwarai suna sanya ƙaunar mutum a zuciyar abokan zamansa da sauran 'yan uwa.


Sau da dama an sha samun asara mai yawa ta rai ko ta dukiya, da ɓacin rai mai tsanani, saboda wani ya kasa haƙuri a samu yadda ake so ko ya yi abin da ya kamata daga bangarensa, don yana ganin ba shi ne zai amfana ba, ko kuma idan ya yi haka zai takura.

Abba Abubakar


E, ba an ce lallai mutum ya riƙa takurawa kansa don jin daɗin wasu ba ne, amma kyautatawa tana da amfani, kuma akwai alheri da ke bin bayan sadaukarwa ta tsakani da Allah. Ba kowanne lokaci ne yin abin da ya kamata ke zama takura ba, sauke nauyi ne. Kai ma wani lokaci za ka nemi wani abu daga wajen wani, wanda ka ke ganin ya kamata ya yi maka, idan bai yi ba kai ma ba za ka ji daɗi ba.


Mutane masu son zuciya ba sa taɓa samun wadata da gamsuwa da rayuwar su, ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da suke so, saboda ko da yaushe tunanin su ba ya wuce jin daɗin kansu ta hanyar ƙuntatawa wasu.


An rawaito a hadisi ma'aikin Allah mai tsira da aminci yana cewa, imanin ɗayanku ba zai cika ba, har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa.


A nan za mu fahimci cewa, ashe kyautatawa don jin daɗin wani ko wasu addini ne, kuma alama ce ta cikar imani. 


Don haka kira na ga mai karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya bacin zuciya!

Reactions
Close Menu