"Marubuta za su fi jaruman fim iya riƙe aure" - Mohammed Umar

Jerin wasu daga tsofaffin jarumai mata na Kannywood da auren su ya mutu.


Malam Mohammed Umar masani ne kuma kuma babban malami a Kwalejin Horar da Malamai ta Jiha dake garin Gashua na jihar Yobe. Manazarci ne dake sharhi kan al'amuran yau da kullum inda kamar kodayaushe a wannan karon ya baƙunci Mujallar ADABI bayan da yayi wani tsokaci gami da fashin baƙi biyo bayan karanta tattaunawar da Mujallar ADABI tayi da marubuciya Fatima Aminu Ya'u wadda ta kasance mazauniyar Kano daga jerin rahotannin mu na makon da ya gabata.


Mohammaed Umar ɗin ya zaɓi yin tsokaci kan wani ɓangare na tattaunawar daga cikin kalaman da marubuciyar inda yayi fashin baƙi daga inda ta bayyanawa Mujallar ADABI cewa babu wani aibu da ita ta gani don marubuciya ta auri marubuci domin zasu fi bada kulawa ga juna. Inda ya fara da yin nuni da cewa shi kan shi auren marubuta a junan nasu ba zai kasance a yadda za a tsammanta ba na cewa zasu kula da juna muddin zahiri da baɗinin su bai kasance ɗaya da abinda suke rubutawan ba kamar yadda yace, 

Ni a fahimta ta, ko da mutum marubuci ne to halayen sa da ɗabi'unsa na zahiri da na baɗini su ne abinda za su iya tabbatar da yadda zai kula da matarsa idan yayi aure...


Masanin ya ɗora ta hanyar bada misali kan yadda yanayin zamantakewar aure na jaruman masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood yake kasancewa da cewa, 

Idan aka dubi masu shirya fina-finai suna ƙoƙarin nuna mu'amala maikyau lokacin zamatakewar su na aure amma dukda haka wasu daga cikinsu sun kasa zama a gidajen mazajen su...

 

Ya kuma ɗorawa da bayanin dake nuni cewa dacewar hayayen marubuta da na abinda suke rubutawan shi ne zai tabbatar da ingancin zamantakewar su yayin da suka yi aure kamar yadda ya furta,

...Saboda haka ni ina ga idan marubucin yana da halayen da suka dace da rubutun da yake yi, zai iya rike mace da amana da kyakykyawar muamala amma idan aka samu akasin haka gaskiya ba lallai ne macen ta samu yadda take so a gidan marubucin ba.


Sai dai a ƙarshe ya rufe batun na shi da kalaman dake nuna aminta da cewa marubuta na iya zarta takwarorin su dake Kannywood wajen iya zamantakewa inda yace, 

Daga ƙarshe, bisa fahimta ta idan aka samu marubuta masu halaye nagari suka yi aure a gefe ɗaya kuma aka samu 'yar fim da ɗan film masu halayya nagari da su ma suka yi aure. Gaskiya marubutan za su fi aiwatar da abinda suka saba rubutawa sama da yadda jaruman fina-finan zasu aiwatar.

Reactions
Close Menu