Mujallar ADABI ta taya Safnah Aliyu Jawabi murna

 

Ɗaukacin ma'aikatan kamfanin dillancin labarai dake wallafa Mujallar ADABI sun yabawa ƙoƙarin marubuciya Safnah Aliyu Jawabi tare da taya ta farin cikin kammala littafinta mai suna "Musaddam Ne Zaɓina" wanda mujallar take wallafawa a shafinta na yanar-gizo.

Saƙon wanda ke ɗauke cikin wata wasiƙar da aka rubuto daga ofishin Babban Edita na Mujallar ADABI, Musaddam Idriss Musa ta fito ne kwana ɗaya bayan kammala littafin mai shafuka 56 a tsari na shafuka irin na marubutan labarai na yanar-gizo.

...kawo wa zuwa wannan lokaci da kika kammala rubutun wannan littafi da kika yiwa laƙabi da suna na kansa wata babbar nasara ce. Dukda cewa kin fuskanci kalubale akan rubuta littafin daga waɗansu, hakan bai sa kin kasa cigaba da rubutun ba....ina matukar alfahari dake ina kuma fatan za ki cigaba da ƙara bada himma a rubuce-rubucen da za ki yi nan gaba. A bisa tarihin da kika kafa a wannan kamfani namu da kuma kwazo da kika nuna wajen rubuta wannan littafi nake sanar dake cewa Mujallar ADABI ta tsara shirin karramaki...

Wasu saƙonni kenan daga abubuwan da wasiƙar ta ƙunsa. Wannan duk ya faru ne a lokacin da 'yan uwa da masoya tare da ƙawayen marubuciyar ke cigaba da tayata murna.

Reactions
Close Menu