Ranar Dimokaraɗiyya: Wasiƙa zuwa ga matasan Najeriya

Tare da Comr. Maliya Isma'il Maliya


Ya ‘yan uwana maza da mata ‘yan Nigeria wannan rana ta yau wato 12 ga Yuni, rana ce ta DIMOKARADIYYA a tarayyar Najeriya. Rana ce wacce ta shafi rayuwar matasan wannan kasa, domin a irin wannan ranar kusan a ita ce ake rusa rayuwarmu mu matasa, kuma a ita ne idan matasa muka yi karatun tanutsu za mu gina rayuwar al’ummar kasar nan a matsayin kasa wadda dukkanin duniya za ake kwatance da ita.

Ya ‘yan uwana matasa lokaci ya yi da ya kamata mu yi watsi da dukkanin masu zuga mu, da mana mummunar huduba, mu shigo mu yi siyasa, mu tsaya takara a kujeru daban-daban domin mu ceto kasarmu da nahiyar Afirka, mu sani daukan makami, yin garkuwa da mutune (Kidnapping), ba su ne abubuwan da za su fidda mu da ga kangin da muke ciki ba, shiga harkar siyasa da yin ta cikin yanayi mai tsafta zai zame mana mafita. Idan mun shiga siyasar mu nemi mukamai, da zarar mun rike ragamar kasar nan Insha Allahu za mu sami damar da za mu gyara kasarmu.

‘Yan uwanan matasa mu sani fa Najeriya kasa ce kamar sauran kasashen duniya, in har mu matasa ba mu tashi mun gyara ta ba, to kada mu yi tunanin samun gyaran ta da ga matasan wata kasar ko kuma kada mu tsammaci mala’iku ko aljannu ne za su gyara mana kasarmu. ‘Yan Najeriya suka bata Nigeria, ‘yan Najeriya ne kuma za mu gyara ta.

Ya ‘yan uwa ‘yan Najeriya ya zama wajibi mu yi aiki da abubuwa kyawawa wadanda addinai suka koyar, addinin Musulunci da ma na Kirista. Allah ya albarkaci kasarmu da masu ilimi da hikima daban-daban kuma ‘yan kisihn kasa, wasu sun mutu wasu suna a raye, dan haka ya na da kyau mu rika bibiyar tarihinsu zai amfanar da mu.Shugabanni na wannan kasa ya zama wajibi a gareku ku ja matasa a jika, ku basu dama domin su ma a dama da su a siyasar wannan kasa. Jan matasan a jika zai sa su ji cewa su ma ‘yan kasa ne an kimanta su, haka zalika jan nasu a jika zai kauda kansu da ga shiga kungiyoyin ta’addanci.

Duk matashin da yake da sha’awar shiga siyasa tabbas ya na da bukatar samun goyon baya da daurin gindi, musamman da ga wajen ‘yan uwansa matsa.

Ya ‘yan uwana matasa mu ajiye dogon buri da kwadayin abin duniya domin hakan shi yake haifar mana da gurbataccen tunani har mu kai ga aikataka aikin ta’addanci ko wani aiki na assha.

Ya ‘yan uwana matasa mu tashi mu hade kanmu karkashin kyakkyawar manufa, domin ceto kasarmu ta hanyar amfani da doron doka da oda, domin gyara kasarmu. Mu sani idan Najeriya ta gyaru mu za mu ji dadi, idan ta lalace mu za mu sha wahala.

Ina yi mana barka da wannan rana ta DIMOKARADIYYA, tare da fatan alheri ga dukkanin al’ummar kasarmu ta gado, Allah ya taimaki kasarmu Najeriya, ya kara tsayarta akan turbar DIMOKARADIYYA bisa hanyar gaskiya da amana.


Rubutun:

COMR. MALIYA ISMA’IL MALIYA

08032725355/08080849227

Reactions
Close Menu