'Sakaci' ƙirƙirarren gajeren labari daga Ahmad Toshiba


SAKACI
°°°°°°°°°°°°°°°°
Na
°°°°°°°°°
Ahmad Toshiba


Dandazon jama'a ne a bangaren da ake duba lafiyar yara kanana wato (Pediatric Clinic) zaune kan kujeru kowa yayi shiru babu mai magana da dan uwansa wasu ma na tsaye rike da 'ya'yansu a hannunsu suna jijjiga su sakamakon kukan da suke ga shi lokacin gari bai gama wayewa ba misalin karfe 6:00 ne na safiya. Da dai alamu mutanen nan asubanci su kayo don zuwa asibitin ga shi su kan su ma‟aikatan bangaren da ake sayar da katin ganin likitan ba su zo ba kuma gurin babu likita ko daya. 


Wata mata ce ta shigo wajen cikin tashin hankali da firgici rike da yaro a hannunta tana zubda hawaye tana tambayar ina ne wajen da ake yankar katin ganin likita, daya daga cikin matan da suke wajen tace da ita.


“Kin ga baiwar Allah tun asubar fari muke nan wajen domin kama layin siyan kati don ganin likita kuma ga shi har yanzu ba su iso ba, sai dai ke ma ki kama layi kawai mu jira su idan sun gama mulkinsu daga gidajensu sa fito su duba mana yara.” 


Wannan mata hankalinta ya dad'a tashi sakamakon yaron dake hannunta sai ja yake dama ta iso da shi baya cikin hayyacinsa haka ta nemi wuri ta zauna akan kujera sai kuka take bayan kamar dakika 30 masusiyar da katin suka iso suka bude ofishinsu da suke sayar da katin duba da halin da matar take ciki da kuma yanayin yadda yaronta yake ciki sai jama'ar wajen suka ce da ita sun daga Mata kafa ita da wata matar su biyu kenan da su siya katin don idan likita yazo ya fara ganin yaransu saboda gaskiya yadda yaran suka jikkata dole a tausaya musu. 


Shigarsu cikin ofishin da ake siyar da katin da shi mutumin da yake sayar da katin ya kalli yaran sai da ya tausaya musu 


“Duba da yanayin yaran nan Bari mu gwada wata dama mana zan je bangaren da ake kallon manya domin neman alfarma da su duba yaran kunnan don gaskiya suna bukatar taimakon agajin gaggawa”


Wadannan mata su kayi masa godiya sosai bisa kokarin taimaka musu da yayi. Ya tashi yayi waje rike da fayil nasu a hannu izuwa shashen da suke kallon manyan mutane wato (General Out Patient Clinic) an kuwa tsinci sa'a ya sami har likitoci mutum hudu suna aiki a wannan shashe sallama yayi musu cikakkiya kana ya samu wuri ya tsaya sai chief (shugaban shashen) yace da shi 


“menene ya kawo ka?”


"Chief wallahi wasu patient ne yara guda biyu suna bukatar agajin gaggawa sakamakon yanayin jikin nasu kuma gashi har yanzu clinic namu Babu likita ko daya" 


Chief din ya kalle shi cikin fada.


“Ina ruwa na ni na hana su zuwa ko so kake mu bar namu aikin muje don mu duba musu nasu marasa lafiyan?” 


Cikin sanyin jiki wannan mai siyar da katin yace dashi a'a haka nan ya kore shi yace dashi ya fita ya bar masa ofishin sa. Ya juya don ya fita, sai wani daga cikin likitocin yace da shi “bari na zo mu je na zauna na duba su kafin naku likitocin su fito sai wannan shugaban na su ya hana shi fita.”


Bayan wannan mutumi ya dawo Cikin nasu ofishin da suke sayar da katin ganin likita ya tarad da wannan Mata guda biyun daya bari aciki ya musu bayanin yadda su kayi ya kuma Basu hakuri akan su jira nasu likitan idan yazo sai ya duba su hakan kuwa su kayi suka tashi suka fita waje zaman jiran zuwan likita ba'a jima ba shi yaro namijin ya fara ja da karfi fiye da yadda yake yi dazu sannan idanunshi duk sun kakkafe waje daya. Allahu Akbar! Ashe lokaci yayi Allah mai yi ya karbi abunsa haka matar nan ta ajiye yaron akan kujerar da suke zaune sai maganganu take na bacin rai cikin fusata nan dai wani likita ya zo wucewa sai ya ji irin maganganun da take shi ne ya tsaya ya dube ta 


"Haba hajiya hakuri za kiyi bai kamata idan Rai ya baci kuma ki rinka maganganu irin haka ba sannan ki sani ba laifin likita kadai za ki gani ba ku ma iyayen yara kuna da naku sakacin wato idan yaro ya fara rashin lafiya baza ku zo asibiti da wuri ba sai dai ku yi zamanku a gida kuna na gargajiya cuta kuma tana ta kara shiga jikin yaro tana girma har sai an zo matakin da kun ga yaro ya galabaita sai ku dauko shi ku nufo mu da shi asibiti wanda mu kuma a lokacin babu abinda za mu iya idan an samu irin wannan kuskuren kuma sai kuyi ta ganin laifin mu kadai, gaskiya ya kamata ku rinka sanin cewa likita shi ma mutum ne irinku duk abunda kuke iya aikatawa na bukata to shi ma yanayinsa.”


Duk jama'ar dake wurin sai jikinsu yayi sanyi da jin bayanan wannan likitan saboda gaskiya ya fada musu

Reactions
Close Menu