"Shigowar ƙabilu ne yasa Kannywood ta lalace" - Kamal Iyantama

A yayin da guguwar iska da hadirin da ya taso ya turnuƙe samaniyar masana'antar Kannywood ke cigaba da haɗuwa inda ake samun ƙananun zantuka da gutsiri tsoma na tasowa daga ɓangarorin wasu da ake ganin suna cikin jerin masu faɗa a ji cikin masana'antar. Mujallar ADABI ta gayyaci fitaccen matashin nan mai baiwar waƙa da rubutu sannan kuma mai fasahar zane-zane wato Kamal Iyantama wanda ya kasance ɗaya daga matasan da suka kwana biyu a masana'antar don tattaunawa da shi wajen gano shin mene ne maƙasudin samuwar matsaloli a masana'antar wanda ya kai ga su waɗanda ke cikin nata ne da kansu suke kukan lalacewar al'amuran cikin ta ɗin a yanzu? Ga hirar ta shi da Mujallar ADABI daki-daki don sanin matsalolin Kannywood, abubuwan da suka haifar da su tare da matakan da za a bi wajen magance su. Ga tattaunawar kamar haka:Mujallar ADABI: Malam Kamal Iyantama muna yi maka maraba. Da farko masu karatu zasu so jin cikakken sunan ka tare kuma da tarihin rayuwarka a taƙaice.


Iyantama: To Alhamdulillah ! Kamar yadda aka sani, cikakken sunana dai shi ne Kamal Yunus bin Abdallah. Ni Musulmi ne dan salin Arewacin Nijeriya, da ya fito daga jinsin ƙabilun Hausa / Kanuri, mazaunin jihohin Katsina da Kano. Ina zaune ko nace na taso a gaban iyayena na yi karatuna tun daga primary har secondary. Yanzu haka kuma ni dalibi ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abdu Gusau Polytechnic, Talata - Mafara jihar Zamfara.


Mujallar ADABI: Ya aka yi ka samu shi wannan laƙabi na "Iyantama"?


Iyantama: To Shi dai wannan suna ko kuma wannan lakabi na IYANTAMA, lallai na samo shi ne daga wurin Yayana, Ubangidana kuma abokin aiki wato fitaccen jarumi, mashiryin fim, darakta kuma furodusa a masana'antar shirya fina - finai ta Kannywood, wato Alh. Hamisu Lamido Iyantama. Haka dai shine shugaban kamfanin shirya fina - finai na IYANTAMA MULTIMEDIA NIG. LTD. To a takaice dai kun ji in da na samo wannan suna ko lakabi.


Mujallar ADABI: Ka kasance mai sana'ar zane-zane, marubucin fim sannan kuma mawaƙi wanda hakan ke nuna kyakkyawar alakarka da masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood. Shin ya za ka bayyana yanayin gamsuwarka kan yadda al'amura ke tafiya a masana'antar?


Iyantama: Hakika lallai na samu kaina ko nace na shigo wannan masana'anta, na sameta ba yadda nake so ko yadda na yi tsammani ba. Dukda kafin na shigo ta gaskiya ydda take abin fahari da tinkaho ne, al'amuranta na tafiya yadda ya kamata, kowa na ta cin abincinsa hankali kwance, babu mai kyashin kowa. Amma gaskiya ina takaicin yadda take a yanzu.


Mujallar ADABI: Idan aka yi duba kan yadda ake samun yawaitar korafi na lalacewar masana'antar a yanzu. Me kake ganin cewa shi ya kai ga janyo taɓarɓarewar al'ummuran?

...batun gaskiya shigowar ƙabilu ne babbar matsalar da ta yi kaka - gida, ta bi ta lalata komai, aka rinƙa ganin ba daidai ba.

Iyantama: Wato ba na ganin aibi ko laifin dukkan wanda zai buda baki ya ce lamuran masana'antar shirya fina - finai sun lalace. tare da tabarbarewa. Don kuwa an ce da ma sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga, to wannan bangon ba ma tsagewa kadai ya yi ba a'a tsatstsagewa ya yi ya ragargaje !. Kuma batun gaskiya shigowar ƙabilu ne babbar matsalar da ta yi kaka - gida, ta bi ta lalata komai, aka rinƙa ganin ba daidai ba.


Mujallar ADABI: Waɗanne abubuwa ne kake ganin cewa su ne manyan matsalolin Kannywood a yanzu?


Iyantama: Eh ! Kamar yadda na fada ma a can baya cewar ; shigowar Kabilu ( 'yan na iya kenan ). Duk da ba na ganin laifi ne in wani dan wata kabila ya shigo wata ƙabila, don yin irin sana'ar da ƙabilar ke yi, matukar ya bi tsari da kuma ƙa'idojin wannan ƙabila, wannan babban ci gaba ne ma. Karka manta sunanta fa masana'artar shirya fina - finan Hausa, to wadannan 'yan na iya din sai suka yi sa'ar shi yaren Hausa yare ne mai dabi'ar nan ta tsuntsun hankaka wato; wanda ke mayar da dan wani nasa, hakan ya basu damar yin yadda suka ga dama, bayan ko da suka zo sun tarar da 'ya'yan cikinta suna tafiyar da harkar cikin tsabta, nagarta da kuma tsari, gwanin sha'awa. To 'yan halaliyar cikinta dai zan iya cewa sun yi farin cikin zuwan wadannan 'yan na iya din, saboda ko ba mi ci gaba ake so a harkar, maimakon su a matsayinsu na baki, su bi tsari da dokokin wannan masana'arta kamar yadda suka tarar, a'a sai suka yi irin abin nan na " wuce makadi da rawa ", duk da masu wannan wuri sun yi masu nuni na kaikace da na zahiri, amma sai suka nuna rashin da'a.

Wannan rashin biyayya ne ya sa su halartattun cikin sai suka tsame hannuwansu, domin ba sa su lamunci sa hannunsu ba a wurin ruguza al'adarsu ba ta Hausa. 

Wannan rashin biyayya ne ya sa su halartattun cikin sai suka tsame hannuwansu, domin ba sa su lamunci sa hannunsu ba a wurin ruguza al'adarsu ba ta Hausa. Yanzu dai ba ki daya abin ya kai makura, matsalolin da ke ciki sun yi yawan da ba a iya lissafasu, kuma su 'yan na iya din sun ki yarda cewar su ne matsalar, duk da din sun san cewar su ne din.


Mujallar ADABI: Ta wace hanya kake ganin za a shawo kan su?


Iyantama: Hanyar dai daya ce tilo ni a ganina fa kenan, wato 'yan na iya su ruga zuwa ga 'yan asalin wannan masana'anta, su durkusa farko su fara da neman gafararsu, sannan su ce to sun zo ne domin a nemo bakin zaren dinke barakar da suka yi. Idan hakan ta samu to da ma abinda ake nema kenan, ka ga komi zai dawo, kuma harkar fim za ta dawo da martabarta a idon duniya.

Reactions
Close Menu