Waƙar Adam A. Zango ta janyo fashewar bom a teburin manazarta ayyukan Kannywood

Jarumi Adam A. Zango a bidiyon wakar zuciya ce tare da Momee Gombe

Wani abu da ba kasafai aka saba lura da shi ba musamman masu sha'awar kallon finafinan Hausa shi ne "duba daidaiton tafiyar abinda baki ke furtawa da kuma yanayi na maganar gangar jiki a sanda furucin ke fitowa". Wannan al'ada ce watakila ta ɗaukacin masu kallo yayin da jifa-jifa kuma akan samu ƙalilan da ke nuna ra'ayin ƙin kallon finafinai da waƙoƙin Hausa bisa dalilan da sukan bar wa kan su. Inda wasu kuma kan ce rashin iya taka rawar jaruman ko wasu abubuwan da sukan yi a cikin shiri ke sosa zukatan su wanda har hakan ke sa suke kauracewa kallon finafinan Hausan suke karkata ga kallon na wasu ƙasashen duniya. Abin tambayar a nan shi ne, shin da gaske ne dukda cigaban da jaruman Kannywood a yanzu ke iƙirarin masana'antar ta su ta samu, har yanzu akwai matsalar rashin kwarewa a tattare da su? Watakila ta hanyar yin tsokacin ku wato 'comment' a kasan wannan post ɗin zai ba mu damar samo amsar tambayar nan.

      Amma kafin nan bari mu je ga rahoton da wakilin mu, Musaddam Idriss Musa ya haɗa mana bayan tashin wani babban bom a teburin jerin gwanon wasu haziƙan marubuta kuma manazarta lamuran da suka shafi Kannywood ɗin kan wata waƙar da Adam A. Zango tare da Momee Gombe suka yi bidiyon ta mai suna, 'ZUCIYA CE'.

    Waƙar mai tsawon mintuna 3:56 wadda matashin mawaƙin nan da a yanzu yake kan sharafin sa wato Auta Mg Boy ya rera, su kuma jarumi Adam A. Zango tare da matashiyar jaruma Momee Gombe suka hau kan bidiyon ta, waka ce da za a iya cewa an rera ta ne da makantacciyar zuciyar da so ya kwaranya cikinta har ya kai ga ɗarsa sassanin bege cike da shauƙin da kusan baki na ba zai iya bayyana shi ba.

Hoton Adam A. Zango tare da Momee Gombe a waƙar zuciya ce

Salon yanayin tafiyar wakar da yadda ta su daddaɗan kiɗa mai taushi da tsuma zuciya kaɗai wani abu ne da ko shi kaɗai ya isa motsa zuciyar ma'abocin so bare kuma uwa uba sanyayan daɗaɗan kalaman da mawaƙin yayi amfani da su. Misali kamar kalmomin da yayi amfani da su wanda suka zamo su ne mabuɗi ga waƙar inda yake cewa:

Zuciya ce, zuciya ce

Sonki ya kama samu gu,

 Cikin ta yayi zaune.

Duk muhalli cikin ta,

Sunanki duk ya zazzane.

Ke ce abar sona,

Sannan muradi na.

Ni dai na yi nisa a so,

Son ki ne zahiri.

In ba ke ba sai rijiya,

'Kin shigan lammari.

Har wayau, baitocin waƙar sun cigaba da jerantuwa kamar haka:

Hoton Adam A. Zango tare da Momee Gombe a waƙar zuciya ce.

Wanda ya so ki kam ni da,

shi ne akwai bugun tambari.

Dole a dau guda daya cikin mu,

Ran nan akai kabbari.

Ko kallonki ban son a na yi,

Indai akanki ne ba na da tausayi.

Sannan a sonki ba na da ra'ayi,

A kalaman so mu ake kwaikwayi....

    Har izuwa inda waƙar ta ƙare. Babban abinda ya jawo hankalin manazarta har suka kai ga yin tsokaci akan ita wannan waƙa shi ne yanayin yadda jarumai biyun wato Adam A. Zango da kuma Momme Gomben suka hau waƙar wadda a bisa nazarin wasu hakan sam bai tafi daidai da tsarin waƙar ba yayin da wasu kuma kan ce, ba wata matsala a yadda suka bayyanar da yanayin nasu. Lamarin da ya janyo jayayya mai ƙarfi kenan inda kowanne yayi tsokacinsa akan wakar.

Hoton Adam A. Zango tare da Momee Gombe a waƙar zuciya ce

Babban abin da ya janyo takfa muhawar shi ne yanayin motsin jikin jaruman musamman ma fuskokinsu wanda suke a ɗaure ba alamar annuri kamar dai waɗanda ke rera waƙar mutuwa a cewar wasu cikin manazartan.

    Bari mu fara da yin duba ga mutum na farko wato Anam Dorayi mazaunin jihar Kano inda ta zamo tushiyar masana'antar ta Kannywood wanda kuma ya kasance marubuci ne kana ƙwararre a harkar canjin kuɗi na yanar-gizo sannan CEO na Ahmed.com wanda ya bayyana ra'ayin sa da cewa;

A mahanga ta, wakar ta yi daidai da wata waƙa da Ita Gomben ta hau, wanda take nuna jimami ga yadda taƙi karbar soyayyarsa a baya. A waccan wakar zan iya tuna wani baiti da yake cewa, "Na yi-na yi nusar da ke a kan son ki zana iya rasa rai na. To wannan ma a farkon gani ni na da ita, sai da na yi mata kallo kusan uku, kafin na ce maka wani abu akai. Abu na biyu kuma, na yi nazarin anya ma wannan waƙar ita suka hau, sai da ƙyar na gano lallai shi ke mamming din. A karo na uku na gane cewa, acting din Jaruman bai dace da wakar ba. Sai ya sanya ni tunani, to ko dole aka yi musu su yi waka a tare. A karshe dai, waƙar ta soyayya ce, amma mawaƙan damuwa suke nunawa. Amma babu abun da zai min alƙalanci, sai kallon waƙar, daga farko zuwa ƙarshe.

Anam Dorayi

Da wakilin namu ya jefa masa tambaya, shin ko hakan na da nasaba da rashin kwarewar aiki ko kuma rashin iya sanya abin a jiki ta yadda komai zai daidai da abinda baki ke furtawa, Dorayin ya ba shi amsa da cewa:

A gaskiya dole na tsayar da abun a kan Zango ɗin shi kaɗai. Kawai abun da na lura a nan shi yanzu ba shi da ra'ayin Film. Ko kuma dai yana jin cewa, duk abin da ya yi daidai ne. Don idan ka kula, a mafi yawa yanzu, shi ba ya fita a film in dai ba nasa ba. Don haka wannan zai sanya cewa, shi ne: Producer kuma Director da duk wani babban role da ke yin ƙokarin gyara a harkar Film. Don haka dole duk yadda ya so ganin Film ɗinsa a bar shi haka. Saɓanin takwaransa, Ali. Shi kullum Tauraruwarsa ce ba ya so ta dusashe. Komai ƙankantar Producer, idan har ya kawo masa aiki, kuma yayi masa alkawarin yin aikin, yana yin iyakar ƙokari wajen ganin Film ɗin ya fitar da ma'anar da ake son aikawa. To a taƙaice wannan na nunar da rashin jagoranci da shugabanci, a masana'antar.

 

Hafeezah Iliyasu Ningi mai sharhi da kuma mai bibiyar harkokin adabi da fina-finan Hausa wadda ta fito daga jihar Bauchi ita ma ta tofa albarkacin bakin ta da cewa:

Yasin yanayin su ya fi kama da bayyana ɓacin rai. Kuma salon tafiyar wakar da yanayin da fuskokinsu suka nuna shi ma bai tafi daidai ba saboda ta yaya an ce waƙar soyayya amma fuska babu annurin soyayya a ciki? Kuma gaskiya rashin iya shigar da abin ajiki ne ya janyo ta yadda furucin da motsin ba sa yin nuni kan abu guda...

 

Saleh Muhammad Daddy

Saleh Muhammad Daddy wanda ya kasance marubuci ne ɗan jihar Yobe ra'ayinsa kenan kodayake sun ɗan saɓa inda yace:

Ba su tafi daidai ba saboda kalaman waƙar suna bayyana farin ciki ne su kuma suna bayyana damuwa ce. Kazalika, rashin iya shigar da abin a jiki ce matsalar amman in dai ƙwarewar aiki ce, ya iya.

 

Fatima Aminu Fayau

Ta gaba a jerin waɗanda wakilin namu ya tuntuɓa ita ce marubuciya Fatima Aminu Fayau daga jihar Kano, wadda ita ma ta shahara sosai a kallon fina-finan gida da na waje. Ga abinda take cewa:

Yanayin jaruman na nuni ne da baƙin ciki da kuma damuwa sannan ko kaɗan acting ɗin su bai tafi daidai da kalaman mawakin ba. Inda kuma rashin ƙwarewa da rashin shigar da aiki inda ya dace, shi ke damun su wanda hakan ya shafi duk jaruman Kannywood ɗin ne gabaki daya. Tun a fara aikin kamata yayi a ce shi kansa mawakin na gurin idan ya ga an yi abinda bai yi daidai da yadda yake jin ya dace da wakar sa ba yayi wa daraktan magana shi kuma ya gyarawa jarumi da jarumar tunda shi ke faɗin me yake son jarumi yayi, duk girman jarumi kuwa.

 

Salahudden Muhammad

Ƙari cikin jerin shi ne marubuci Salahudden Muhammad daga jihar Kaduna wanda ke da ra'ayin da a tashin farkon yayi daidai da na sauran amma a ƙarshe ya saɓa da su inda ya nuna cewa: 

Fuskokin jaruman sun bayyanar da damuwa ne kuma yanayin da suka nuna na fuskokin nasu da kalaman da aka yi a wajen, shakka babu sun daidaitu. Ina kuma kyautata zaton cewa acting ɗin ya tafi daidai da yadda ake so.

 

Amina Ma'aji (Maman Khairat)

Ita ma Amina Ma'aji wadda aka fi sani da Maman Khairat kuma marubuciya daga jihar Yobe da Mujallar ADABI ta nemi jin ra'ayin ta cewa tayi:

Yanayin tafiyar motsin jaruman da fuskokin su ya bayyanar da cewa a cikin damuwa suke.

 

Ahmad Toshiba

A ƙarshe marubuci Ahmad Toshiba shi ma ya bayyana cewa waƙar sam ba ta hau da yanayin ba sannan rashin iya shigar da abun a jiki ne matsalar jaruman.

Shin ya kuke kallon ra'ayoyin manazartan, sun yi daidai da fahimtar ku ko kuwa? Sanar damu a ƙasa inda aka rubuta comment.

Reactions
Close Menu