Waƙar Hannunka Mai Sanda

 

Hannunka Mai Sanda

Na

Ibrahim Khalil


Bissimillah Ya Allah daya,

Ka yi min afuwa Sarki daya,

Zan yi wake in fadi gaskiya,

  Ka tsare karya yau ko gaba.


Yi salati ga Khairul Anbiya,

Mahmudu madubin tafiya,

Sahabu Ahlul baiti gaba daya,

 A salatin ni ban cire su ba.


Hannunka mai sanda zana yi,

Don kasar mun fada yanayi,

Wasu sun rasa ma me za su yi,

 Tsananin wahala ga fargaba.


An haife ni a gidan kasa,

Na zamto mai kishin kasa,

Mai bin dokar wannan kasa,

  Masu sa dokar basu bita ba.


Komai a Arewa bai samu ba,

Yunwa dayawa basu koshi ba,

Ga tsaro sam bai canzu ba,

  Shi talauci ya zama jagaba.


Mun yi zabe kun ce mu yi,

Kun ci zaben gamu a yanayi,

Mun kuka wai mai kuka yi,

  Sai kace sam ba wani shugaba.


Dau batun yunwa na karuwa,

Ga rashin aiki na nunkuwa,

Mutuwar aure na faruwa,

  To,ina wani zancan cigaba.


Babu cin yau balle gobe ma,

Ba kudi koda na sayan rama,

Talaka a yau ya tsunduma, 

  Wani hali da bai san kansa ba.


Ina batun ilimi bai samu ba,

Batun arhar ma bata wanzu ba,

In kadau taki ba su bamu ba,

  Ya batun noma zai kai gaba.


Alkawar duk ba ku cika su ba,

Kun fa rantse in ba ku zauku ba,

Rantsuwar ba za ta fa barku ba,

  Za ta bi ku ta nuna nan gaba.


Kun ci bashi akwai ranar biya,

Za ta zo ta mu dai dada tafiya,

Wata rana dare ne kodai safiya,

  Rabbi zaya saka baku fargaba?


A Arewa ana ta zubar jini,

Al'umma sun fada razani,

Mun zamto bamu da kwar jini,

 Duk mun rasa mai muka sa gaba.


A Kaduna a sace al'umma,

Fansa ita ce kuma lalama,

Abiya su abin ya girmama,

  Su kira ka sunai ma shagaba.


Abin shanya ku sani duka,

Shi da rana wa yafi daukaka,

Kadda ma ku fadamin ya haka,

  Ga iri gona ta zamto jagaba.


Babu ruwa ina shuka kuma,

Ba gona ya noma kuma,

Ba kuri'a ina zaben kuma,

  Talakawa tushen shugaba.


Duk jan manja zaki babu dai,

Shi farin rogo ba kitse ba dai,

Hagen dala ba fa gari ba dai,

 Hattara ku yi domin nan gaba.


Amfaninsa ruwa wanka da sha,

kusani na ibada ya saba da sha,

Don na sirki shi ma za'a sha,

 A fage na ibada ba zai karbu ba.


Ba a fadawa falke tafiya,

Shi rago karfinsa a fariya,

Jarumta jigo ce gun tafiya,

  Nan kasar jarimi bai samu ba.


In ka ji washi kaifi baiyi ba,

A tsaya sagudun bai zo shi ba,

Karya ga malam bata karbu ba,

  To ina mafitar mu a nan gaba?.


A batun kyau a zabo fari,

Shi ko gwarzo sam baya bari,

Mai gaskiya a gan shi da wuri,

  Ba shi bukatar nuni ka ji ba.


Yunwa wahala na karuwa,

Tsanani yana dada yaduwa,

Masu mulki sun shiga dimuwa,

  Ku jira wata rana nan gaba.


Ance talaka ya karo hakuri,

Ita yunwa ta wuce jinkiri,

Ba ta bukatar kayan marmari,

 Ga shi koda kunu bamu koshi ba.

Reactions
Close Menu