Waƙar 'Ummulkhairi' daga Muhammad Musa Tika

Sunan waƙa:

UMMUL-KHAIRI

Marubuci:

Muhammad Musa Tika

~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~

Al-maliƙu sarki shi daya,

Mai mulkin dukkan duniya,

Ban basira Rabbi da kariya.

Nayi waƙen so ba tutiya,

Ga abar faharina gimbiya.


Ummul-khairi saurauniya,

Sahiba a garen me tarbiya,

'Yar fara tamkar zinariya

Me kyan fuska da na zuciya.

Babu ja kan k'iranki da gimbiya.


Na amince na rasa dukiya,

Matukar ba ke habibiya,

Dawisu gwana gun kwalliya,

Son ta ya kama min zuciya,

Tallafa karki barni na sha wuya.


Son ki yabi jini ya zagaya,

Ya shige min sassan zuciya,

Na kasa tsaye ko zauniya,

Ke nake son kallo kulliya,

Juna mu r'ike ba shariya,


Zak'in muryarki kamar zuma,

Kaunarki a rai naka girmama,

Zo ki jamin dukkan ragama,

Kiyi taku na ki a lalama,

Me farar aniya annuriya,


Fagen ilmu ba a barki ba,

Hakali ni banga kamarki ba,

Mata kece a sahun gaba,

Ayyukan khairi kika sa gaba,

Yadda na baki gaba d'aya.


Ba dare rana kuji yan'uwa,

Kaunarta yana dada k'aruwa,

A zuci yake dada ruruwa,

Darajarta yana dada hauhawa,

A baki da zuciya bai daya.


Da rashin kallonki masoyiya,

Gara inshiga kogin maliya,

Ko na tauna ice na madaciya,

A maraice da rana da safiya.

A rashin ki kwarai zan sha wuya.


Dan Musa da Tika gwaninki ne,

Kyan halinki a yau naka zayyane,

A cikin wak'en na bayyane,

Yadda so kaunarki ya mamaye,

Zuciya da jini har jijiya.

Reactions
Close Menu