"Akasarin masu fassara finafinan Indiya ba su ƙware ba" - Bashir Tunusiya

Daga Abba Abubakar Yakubu

Bashir Tunusiya matashi ne ɗan gwagwarmaya da ke fafutuka don wayar da kan matasa wajen yaƙi da munanan ɗabi'u, inganta sha'anin tsaro da samar da zaman lafiya. Ya kasance marubuci kuma masanin harsuna, mai kishin tarihi da al'adu. A tattaunawar sa da ABBA ABUBAKAR YAKUBU matashin ya bayyana yadda yake ba da gudunmawa wajen koyar da harshen Indiyanci da sha'awar sa ta rubuce rubucen littafin adabi. Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance:


Hoton Bashir Tunusiya cikin shigar Indiyawa


ADABI: Ko za ka gabatar mana da kan ka?


TUNUSIYA: Sunana Muhammad Salman Mika'il, amma an fi sani na da Basheer Tunusiya. Na samu wannan suna ne Tunusiya bayan buga wata gasar ƙwallon ƙafar nahiyar Afrika a kasar Tunisia, inda na goyi bayan 'yan wasan Nijeriya da na Tunisia. To, daga nan ne wani yayana ya laƙaba min sunan, kamar wasa ga shi ya bazu har ya yi ƙarfi sosai cikin duniya.ADABI: Wanene Bashir Tunusiya?TUNUSIYA: Basheer Tunusiya, matashi ne ɗan gwagwarmaya, ɗan jarida mai zaman kansa, kuma malamin makaranta. Sannan ya kasance mai sharhi a kafafen watsa labarai kan al'amuran da suka shafi harkokin matasa da son cigaban su.ADABI: Wacce baiwa ka ke da ita wacce ta bambanta ka da sauran matasa?TUNUSIYA: To, a gaskiya zan iya cewa, ina da wata baiwa da Allah Ya bani wanda ba kowanne matashi ba ne za ka samu yana da ita yanzu, wato ina da baiwa ta binciken tarihin magabata da irin gudunmawar su, nasarori da kurakuran da ba a rasa ba, wanda suka aikata. Sannan Allah Ya bani baiwar rashin tsoro, da fahimtar wasu harsunan da ba nawa ba, musamman harshen Indiyanci.ADABI: Mai ya baka sha'awa har ka koyi harshen Indiya?
TUNUSIYA: Da farko na taso a gidan mu babu finafinan da ake kallo sai na Indiya, hakan ya sa na tashi da kallon su har ta kai abin ya shiga raina sosai. Daga nan na fara tunanin yadda zan fara fahimtar harshen, don na riƙa gane maganar su kai tsaye, da samun sauƙin fahimtar fim ɗin. Na fara ne da kalmomin gida na iyaye da 'yan uwa, kamar Bhai (ɗan uwa) Ma (mahaifiya) Pita ko Papa ko Pita-ji duk suna nufin Mahaifi ne da sauran ƙananan kalmomi na hira maganganu na yau da gobe. 


Hakan ya sa na fara fahimtar harshen da ƙara min ƙaimin cigaba da koyon harshen, ta inda har na fara shiga sinima a nan Jos, kuma ina kashe lokuta masu tsada wajen neman yadda zan samu ƙwarewa a kan fahimtar harshen. Har kuma Allah ya haɗa ni wasu abokai masu jin harshen Indiyanci su ma, inda duk lokacin da muka hadu ba ma yin gaisuwa da Hausa sai da Indiyanci, kuma har yanzu hakan muke yi. 


Mein buhot dhanyavaad patrakaar ( ina matuƙar godiya ɗan jarida).ADABI: Wacce gudunmawa ka bayar wajen yaɗa wannan harshe da koyar da shi ga Hausawa masu irin ra'ayin ka?TUNUSIYA: Na yi ƙoƙarin rubuta wani ƙaramin littafi don samun sauƙi ga Hausawa masu ra'ayi irin nawa, kuma littafin ya shiga hannun su sosai. Sannan na kan zauna na fassara waƙa ga abokaina masu son wannan harshe, domin tsinto kalmomi da aike ma budurwa saƙon soyayya da kalaman sace zuciya masu sauƙi, kuma fassarar na sa nishaɗi sosai, yayin jin waƙar, tun da mutum yana fahimtar mai ake faɗa a ciki. Yanzu haka ma ina cigaba da ƙoƙarin sake tsarin littafin don fitar da shi a karo na biyu. 


Mein buhot buhot khushi ho Saab (ina farin ciki sosai sosai, ranka ya daɗe).


Za ka iya sauƙe manhajar Mujallar ADABI yanzu ta wannan link

ADABI: Kana da fatan wata rana ka ziyarci ƙasar Indiya ko samun damar karatun harshen Indiyanci a can?TUNUSIYA: Eh, sosai ma kuwa! Gaskiya ina da burin zuwa ƙasar Indiya don samun damar ƙaro ilimin harshen Indiyanci. ADABI: Shin bayan abokan ka Hausawa masu sha'awar harshen Indiyanci, ka taɓa haɗuwa da wani ɗan ƙasar da ku ke mu'amala tare da shi har ka ƙara inganta naka Indiyancin?TUNISIYA: E, babu shakka na taɓa haɗuwa da wasu matasa 'yan asalin Indiya a Kano, a wani otel, kuma mun yi hira sosai da su, amma da yake abin nasu ne sai da muka haɗa da turanci, kuma muka zama abokai a shafin sada zumunta na Facebook, ta inda suke ƙara min ilimi akan harshen nasu. Har yanzu muna tare, don ko bayan da na rubuta littafin koyon harshen Indiyanci sun taimaka wajen ƙara tallata ni musamman a shafukan su, kuma na samu yabo sosai a wurin 'yan kasar.
ADABI: Yaya ka ke kallon masu harkar fassara finafinan Indiya zuwa Hausa, shin kai ma kana ba su gudunmawa ne?TUNUSIYA: E, gaskiya suna ƙoƙari sosai, don hakan yana taimakawa masu kallo wajen fahimtar mai fim ɗin ke nunawa. Sai dai wani lokaci wasu na fassara finafinan ne da ka kawai, ta inda za su samu kuɗi ba wai don haka ainihin ma'anar fim ɗin take ba.


E, ina ba da gudunmawa wani lokaci idan sun buƙaci hakan, ta hanyar fassara wani sashi na fim idan suka nema a taimaka musu.ADABI: Ta yaya ka samu kan ka a matsayin marubuci?TUNUSIYA: Na samu kaina a matsayin marubuci ne ta hanyar binciken tarihi, sannan kuma na zama malamin makaranta mai koyar da darasin gwamnati, kuma na tsinci kaina a matsayin mai sharhi a gidajen rediyo. Waɗannan dalilai su suka jawo hankalina na zama marubuci, domin shi rubutu shi ne cikakkiyar hujja kuma ginshiƙin ilimi. Sannan karatun da na yi a kan aikin shi ma ya taimaka min wajen kara jan hankalina ga harkar rubuce rubuce.ADABI: Kawo yanzu littattafai nawa ka wallafa?
TUNUSIYA: Na rubuta littattafai kaɗan da basu wuce biyar ba, akwai wasu kuma suna hanya, kuma littattafan sun yi tasiri sosai, domin kuwa sun shiga hannun waɗanda ake so su je, wato dalibai, kuma sun karɓu a wurin su.


Daga cikin su akwai wanda na rubuta da turanci da kuma na Hausa. Ka ga akwai DECENCY IN ISLAM, DRUGS AND DRUG ABUSE, RASHIN TSARO TUSHEN LALACEWAR KASA, MU KOYI INDIYANCI A HARSHEN HAUSA sai kuma MATASA A YAU.ADABI: Yaya ka kalli rayuwar matasan mu wajen halayyar karatun littattafai, kuma yaya za a farfaɗo musu da kwaɗayin son karatu?


TUNUSIYA: Gaskiya matasa yanzu ba sa karatun littattafai, shi ya sa ilimi ya guje musu sosai. Sun fi karanta rubutun ban dariya ko labaran soyayya, ba su damu da duba littattafan da zasu samu ilimi a ciki ba. Sannan a hakan ma sun fi mayar da hankali ga karatun turanci, domin sun raina harshen su na Hausa. Wannan ma ya taka rawa sosai wujen sa matasa su guje wa karatun littattafai. 


Ina ganin ya kamata a samar da wata hanya ta farfaɗo da yadda matasa za su koma karanta irin wadannan littattafai. Kuma ina mai ra'ayin ganin an samar da darussan da za su koyar da su harsunan su na gado, kamar Hausa da sauran manyan harsunan Nijeriya a makarantun sakandire, da koyar da su sanin tarihi da al'adu. Ina ganin ta waɗannan hanyoyi ne za a sanya wa matasa kwaɗayin karanta littattafai. 


Sannan wani babban ƙalubale da ke ƙara gurgunta harkar ilimi a ƙasar nan shi ne, batun sayen amsoshin jarabawa, ko kuma yadda wasu masu makarantu ke yi su riƙa ba da toshiyar baki, don hana jami'an kula da harkokin jarabawa sa ido kan ɗalibai, domin malamai su shiga suna ba su satar amsa. Wannan ba ƙaramin ci baya ba ne a harkar ilimi. 


Ba na mantawa, lokacin da na rubuta wata jarabawar kammala ƙaramar sakandire wato JSSCE na amsa wata tambaya a darasin Hausa, wanda a dalilin yawan karance karancen littattafan da nake yi ne na ilimantu da amsar, sakamakon wani littafi da na karanta a gidan mu cikin littattafan mahaifina.ADABI: Kana da sha'awar faɗaɗa rubuce rubucen ka a kan harkar Adabin Hausa nan gaba?TUNUSIYA: Sosai ma kuwa nan gaba kaɗan ina da burin mayar da alƙiblar rubuce rubucena su koma na labaran adabin Hausa, domin amfani da hanyoyin hikima da nishaɗantarwa wajen isar da saƙonni. Babu shakka Hausa harshe ne da nake alfahari da shi sosai, wani lokaci na kan nuna babu wani harshe da nake ji idan ba Hausa ba.ADABI: Menene burin ka nan gaba a harkar rubuce rubuce?TUNUSIYA: Gaskiya burina shi ne na zama babban marubuci da duniya za ta yi alfahari da shi, kuma na kasance wanda ake bibiyar rubuce rubucen sa a duk inda ake amfani da harshen Hausa a faɗin duniya.ADABI: Wacce karin maganar Hausa ce ke tasiri a rayuwar ka?TUNUSIYA: Ranka ya daɗe, akwai karin maganar da take tasiri kullum a rayuwa ta ita ce kuwa, YAU DA GOBE TA WUCE WASA! Wannan karin maganar tana tayar min tsimi sosai.ADABI: Mun godeTUNUSIYA: Ni ne da godiya, yallaɓai.

Reactions
Close Menu