Al'adu 10 dake zama banbaraƙwai ga wanda ya ji su a karon farko

 


Al'ada ita ce cikar kamalar kowace al'umma domin kuwa tafarki ce da rayuwar mutane ke shifiɗuwa a kai wanda hakan har ma yasa duk al'ummar da ba ta da al'ada ba a yi mata kallon cikakkiyar al'umma. Sai dai kuma akwai rabe-raben da al'ada take da shi ba ya ga na kasa ta izuwa ga al'adar gado ma'ana al'ada irinta gargajiya wadda mutane ke gada tun zamanin kaka da kakanni da kuma al'ada irin wadda zamani ke shigowa da ita. A cikin jerin waɗannan al'adu ne kuma ake samun al'adu masu kyau da kuma al'adun da suka kaucewa hanya. 

Kazalika, tattare da hakan ne kuma ake da al'adu masu ban mamaki ga waɗanda suka kasance ba al'adar su ba.


A wannan rubutun, an yi ƙoƙarin leƙawa cikin al'adun wasu al'ummu daga sassa daban-daban na duniya don gano shin wace al'ada suke da ita wadda idan na waje ya ji sai tadda abin yayi masa banbaraƙwai wataƙila saboda faffaɗan bambancin dake a tsakanin al'adar ta su da kuma irin yadda tasa take. Ƙasa jerin wasu daga manyan al'ummun duniya ne da kuma irin wannan al'ada ta su.


1. A ƙasar Uganda, daga lokacin da 'ya mace ta fidda wanda take so da aure har ta kai shi gidan su, za ta daina cin kaza. Wannan al'ada ce ga duk wanda ya fara jin ta a karon farko zai ji ta banbaraƙwai.2. A ƙasar Birtaniya suna da wata al'ada na hana mutum ɗora hanunsa bisa teburi da nufin hutu yayin da yake a zaune kan kujera.


3. Al'ummar Karai-Karai da ƙasar su ke yankunan jihohin Bauchi, Yobe, Jigawa da wasu sassa na jihar Gombe a Najeriya su ma suna da wata al'ada na cewa idan yaron dake koyon magana ya fara ambaton sunan wani a cikin gida wato danginsa saɓanin sunan mamansa ko na babansa. To wannan da yaron ya buɗi baki da kiran sunan nasa dole ya saya wa yaron kaza.


4. A Ghana, akwai al'adar da ta nuna mace ba za ta iya sayar da kare ba hakanan amfani da kuɗin karen da aka sayar.


5. Hausawan Najeriya ma na da al'adar cewa mace ba za ta yanke farce ko yin kitso da dare ba.6. Hakanan a tsakanin mutanen Ghana akwai al'adar dake hana mata ɗaga kai da dare don kar suna ganin wata.


7. Al'ummar Kanuri ma suna da al'adar hana 'yan mata ƙunshi da kwanannen lalle.


8. A ƙasashen Larabawa nan ma akwai al'adar dake hana buɗe hannayen almakashi idan ba aiki za a yi da shi ba.


9. Ƙabilar konkombas na ƙasar Ghana suna da wata al'ada na musanyar mata. Idan wannan ya ba wa wannan ƙanwarsa ya aura, sai shi ma ya ba shi tasa ƙanwar a yi canje.


10. A Kenya akwai al'adar da ta nuna cewa uba ne kawai a gida yake da ikon yin fito.


Shin kuma kuna da naku al'adun wanda jin su zai sa mutum ya ji abin a matsayin baƙon abu? Ku rubuto mana don a adireshin mu na email a: mujallaradabi@gmail.com

Reactions
Close Menu